Dan Takarar Gwamna Ya Nakasa Jam’iyyarsa Bayan Watsi da Ita Ana Daf da Zabe, Ya Fadi Dalili

Dan Takarar Gwamna Ya Nakasa Jam’iyyarsa Bayan Watsi da Ita Ana Daf da Zabe, Ya Fadi Dalili

  • Ana daf da gunadar da zabe a jihar Edo, dan takarar gwamna a jam’iyyar LP, Azehme Azena ya yi murabus
  • Dan takarar ya mika takardar murabus din ga shugaban LP a karamar hukumar Etsako ta Gabas
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a watan Satumba mai zuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo – Dan takarar gwamnan jihar Edo a jam’iyyar LP, Dakta Azehme Azena ya watsar da jam’iyyarsa ana daf da gudanar da zabe.

Dan takarar ya sanar da hakan ne a yau Asabar 27 ga watan Janairu inda ya mika takardar ga shugaban LP a karamar hukumar Etsako ta Gabas.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki ya sake faruwa a Ibadan yayin da gobara ta tashi a ofishin INEC, an yi karin bayani

Dan takarar gwamna ya yi murabus ana daf da zabe
Dan Takarar Gwamnan LP a Edo, Azena Ya Yi Murabus. Hoto: Azemhe Azena.
Asali: Facebook

Mene dalilin yin murabus din?

Azena wanda ya ke cikin ‘yan takara 18 a zaben da za a gudanar ya soki makudan kudaden siyar da fom din da jam’iyyar ta saka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, jam’iyyar LP ta sanar da kudin siyan fom din takarar gwamnan har naira miliyan 30 a jihar, cewar Tribune.

Dan takarar tun farko ya nuna sha’awar tsayawa takara a zaben wanda za a yi zaben fidda gwani a ranar 22 ga watan Faburairu.

Rahin mutunci da aka masa

A cikin takardar murabus din nashi, Azena ya bayyana rashin jin dadinsa kan rashin adalci da aka yi masa da magoya bayansa.

Ya ce shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Akoko-Edo, Michael Onaivi ya ci mutuncinsu yayin ziyara a a yankin.

Ya kara da cewa Onaivi ya hana shi tare da magoya bayansa shiga karamar hukumar wanda hakan ya yi tasiri a yanke shawarar tashi.

Kara karanta wannan

A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa

Ya ce:

“Na yanke shawarar ce saboda rashin mutunci da aka min yayin yawon siyasa a yankin Edo ta Arewa bayan dukkan wahalar da na sha a jam’iyyar.
“Abin mamaki shugabannin karamar hukumar Akoko-Edo da shugabanta, Michael Onaivi ya dakatar da ni da magoya baya na shigarta.”

Azena ya ce ya kai rahoton abin da ya faru ga uban njam’iyyar a mazabar Edo ta Arewa, Chris Ighodalo amma abin a banza, cewar Daily Post.

Hadimar gwamna ta yi murabus

Kun ji cewa, hadimar Gwamna Godwin Obaseki ta yi murabus a jiya Juma’a 26 ga watan Janairu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarah Ajose-Adeogun ta yi murabus din ne saboda wasu matsalolin cikin gida a gwamnatin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.