Jerin Canji 5 da Za a Gani Kafin Zaben 2023 Idan Kudirin Majalisa Ya Zama Doka

Jerin Canji 5 da Za a Gani Kafin Zaben 2023 Idan Kudirin Majalisa Ya Zama Doka

  • Da zarar 'yan majalisar wakilan tarayya sun yi nasara a kudirinsu, yadda ake shirya zabe zai canza a Najeriya
  • An gabatar da kudirin da zai yi tasiri a ranakun da ake shirya zabe da yadda mutane za su iya kada kuri’arsu
  • Idan an kammala muhawara kuma an amince da kudirin, za a mika shi gaban shugaban kasa domin ya sa hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

FCT, Abuja - ‘Yan majalisar tarayya sun fara wani kokari domin ganin an yi wa dokar zabe wasu kwaskwarima a halin yanzu a Najeriya.

Premium Times tayi nazarin kudirin, ta jaro sauyin da za a samu idan har aka yi nasara.

Zabe a Najeriya
Mutane su na zabe a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Za a sake taba dokar zabe?

Kudirin zai yi garambawul ga dokar zaben da Mai girma Muhammadu Buhari ya sa rattaba hannu a kai a lokacin ya na karagar mulki.

Kara karanta wannan

‘Dan siyasa ya hakura da kujera, saboda magudi aka shirya domin ya lashe zaben majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu canji ake neman a kirkiro a zae?

1. Zabe a rana guda

Ana so a taba sashe na 28 na dokar zabe ta yadda za a iya shirya zaben shugaban kasa, ‘yan majalisa da na gwamnoni a rana guda.

2. Aika sakamakon zabe

Kudirin yana so a wajabta aika sakamakon zabe ta na’ura. Kafin a yi wannan sai an yi garambawul ga sashe na 60 (5) na dokar zaben.

3. Gyara rajistar zabe

Rahoton ya ce ana so hukumar INEC ta rika sabunta rajistar masu zabe duk bayan shekaru 10 domin cire sunayen wadanda suka rasu.

4. Takaita korafin zabe

Cikin burin 'yan majalisar shi ne a hana shigar da korafi na babu gaira babu dalili a kotu bayan zabe, za a iya fara hukunta masu yin hakan.

5. Hana yin zabe babu tantancewa

Idan an yi na’am da yin kwaskwarima ga wani bangaren sashe na 47 na dokar, ba za ta yiwu mutum ya kada kuri’a ba har sai an tantance shi.

Kara karanta wannan

Aiki na shine na biyu mafi wahala a duniya, Gwamnan CBN Cardoso

Za a canza tsarin mulkin Najeriya?

Wasu ‘yan majalisa sun kawo kudirin canza salon mulkin Najeriya daga shugaban kasa zuwa Firayim Minista kamar yadda aka rahoto a baya.

Idan aka koma amfani da tsarin Firayim Minista, za a rika nada ministoci ne daga cikin ‘yan majalisar tarayya akasin tsarin Amurka da aka aro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng