Ganduje Ya Yi Wa PDP Illa Yayin da Babban Jigo a jam'iyyar Ya Koma APC
- Jam’iyyar PDP reshen jihar Ebonyi ta yi babban rashi na ɗaya daga cikin jiga-jiganta zuwa jam’iyyar APC da ke mulki a jihar
- Peter Ede ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP, kuma ya koma tsohuwar jam’iyyarsa, inda ya bayyana dalilinsa na cewa ya gamsu da salon mulkin APC
- Tsohon ɗan majalisar mai ƙarfin faɗa a ji ya kuma koma APC tare da ɗimbin magoya bayansa na jam'iyyar PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ebonyi - Wani jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon ɗan majalisar wakilai wanda ya taɓa wakiltar mazabar Ezza ta Arewa/Ishielu, Peter Ede, ya koma jam’iyyar APC a jihar Ebonyi a hukumance.
A ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu, Peter Ede ya jagoranci ɗimbin magoya bayansa a jam’iyyar PDP zuwa APC, a wani taron da ya gudana a sakatariyar jam’iyyar ta jihar da ke Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.
Me yasa tsohon ɗan majalisar ya fice daga PDP zuwa APC?
Kamar yadda gidan jaridar Channels TV ya ruwaito, tsohon ɗan majalisar ya yi alƙawarin taimakawa wajen samar da yanayi mai kyau domin ci gaban jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ede ya bayyana cewa ya ɗauki matakin komawa jam’iyyar APC ne a jihar Ebonyi saboda manufofin ci gaban jama’a na jam’iyyar mai mulki, rahoton Naija News ya tabbatar.
Da yake karɓar sabbin mambobin a ofishinsa, shugaban jam’iyyar na jihar, Stanley Okoro-Emegha, ya bayyana farin cikinsa da kuma shirin yin aiki da su, yayin da ya bayyana shawarar da suka yanke a matsayin abin farin ciki.
Ya kuma ba su tabbacin cewa za ba za a nuna musu bambanci ba, tare da lura da cewa jam’iyyar a shirye take ta karɓi duk wani mai shirin shigowa cikinta da zuciya ɗaya.
Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ƙaduna, Mukhtar Ramalan Yero, ya sauya sheƙa zuwa APC.
Ramalan Yero ya koma APC ne ƴan watanni kaɗan bayan sanar da cewa ya fita daga jam'iyyar PDP wacce ya riƙe muƙamin gwamna a ƙarƙashinta.
Asali: Legit.ng