Kano: Hankalin Kwamishinoni Ya Tashi Bayan Wa'adin da Abba Kabir Ya Ba Su Ya Cika, Bayanai Sun Fito
- Kwamishinoni a jihar Kano sun shiga tashin hankali bayan ba su wa'adin rubuto ayyukansu kan kujerun da suka rike
- Gwamnan ya bai wa dukkan kwamishinoninsa wa'adin kwanaki 10 kacal da su rubuto masa ayyukan da suka yi a ofisoshinsu
- Wannan na zuwa ne bayan shafe watanni takwas da gwamnan ya yi a kan madafun ikon jihar tun a watan Mayun 2023
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bai wa Kwamishinonin jihar wa'adi kan ayyukan da suka aikata.
Gwamnan ya bai wa dukkan kwamishinoninsa wa'adin kwanaki 10 kacal da su rubuto masa ayyukan da suka yi a ofisoshinsu.
Wani umarni Gwamna Abba Kabir ya bayar?
Hadimin gwamnan a bangaren yada labarai na zamani, Hassan Tukur Sani shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba Kabir ya yi hakan ne don sanin wadanda za a iya ci gaba da tafiya da su a cikin Gwamnati tare da duba kokarinsu.
Wannan na zuwa ne bayan shafe watanni takwas a kan madafun ikon jihar wanda ya karbi rantsuwa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Tun farko daman gwamnan ya bayyana hakan
Idan ba a mantaba, tun ranar da ya nada kwamishinonin ya tabbatar musu da cewa nadin nasu na watanni shida ne kacal.
Gwamnan ya ce zai duba ayyukan ko wane daga cikinsu bayan watanni shida don duba yiwuwar ci gaba da aiki da shi ko rasa mukaminsa.
Hakan zai taimaka wurin zakulo wadanda suka yi aiki tukuru don ci gaba da aiki tare da su.
Yan kasuwa sun rage kayan masarufi
A baya kun ji cewa, - Yan kasuwar da ke siyar da kayan masarufi wadanda mutane ke amfani da su yau da kullum sun yanke shawarar rage farashin kayayyakin su a jihar Kano.
Shugaban 'yan kasuwar, Ibrahim Ɗanyaro shi ne ya bayyana haka yayin hira da 'yan jaridu jim kadan bayan ganawa da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da al'umma Najeriya ke cikin wani irin mawuyacin hali na tsadar kayan abinci da matsin rayuwa.
Asali: Legit.ng