Tsadar Rayuwa: Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Matakin Tinubu Na Fitar da Abinci, Ya Roki Jama’a

Tsadar Rayuwa: Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Matakin Tinubu Na Fitar da Abinci, Ya Roki Jama’a

  • Tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yabawa matakin Tinubu na samar da sauki a kasar
  • Kwankwaso ya ce fitar da tan dubu 102 na kayan abinci zai taimaka wurin dakile tsadar abinci a Najeriya
  • Ilyasu ya bayyana haka ne a yau Asabar 10 ga watan Faburairu yayin hira da ‘yan jaridu a Kano inda ya bukaci a kara hakuri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano, Ilyasu Musa Kwankwaso ya yabawa matakin fitar da abinci da Shugaba Tinubu ya yi.

Kwankwaso wanda tsohon kwamishina ne a jihar ya ce fitar da tan dubu 102 na kayan abinci zai taimaka wurin dakile tsadar abinci.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Kwankwaso ya yi magana kan matakin da Tinubu ya sauka kan tsadar rayuwa
Ilyasu Kwankwaso Ya Yabawa Tinubu Kan Matakin Fitar da Abinci. Hoto: Bola Tinubu, Ilyasu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Mene Kwankwaso ke cewa kan Tinubu?

Ilyasu ya bayyana haka ne a yau Asabar 10 ga watan Faburairu yayin hira da ‘yan jaridu a Kano inda ya bukaci a kara hakuri da Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Shugaba Tinubu ya na sane da dukkan kuncin da ‘yan kasar ke ciki na matsin tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa, cewar Tribune.

A cewarsa:

“Ya kamata ‘yan Najeriya su godewa Allah da ya ba su Tinubu a matsayin shugaban mai jin kokensu.
“Ya ce fitar da tan dubu 102 na masara da gero daga Baitul Mali zai taimaka wurin dakile tsadar abincin a kasar.

Shawarar da Kwankwaso ya bayar

Kwankwaso ya ce ma’aikatar noma ta na kokarin samar da tan dub 42 na masara da gero da kuma gari don saukaka wa mutane.

Ya ce har ila yau, ‘yan Najeriya ya kamata su sani tsadar abincin ba laifin Shugaba Tinubu ba ne illa hauhawan dala wanda ya ke kokatin dakilewa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya tura sako ga Hukumar ICPC kan boye abinci, ya dauki alkawari

Ya kushe matakin jam’iyyar adawa ta PDP inda ta caccaki tsarin da Bola Tinubu ya dauko don dakile tsadar rayuwa da ake ciki, Independent ta tattaro.

‘Yan kasuwa sun koma ga Allah

Kun ji cewa yayin da ake cikin matsanancin halin matsi, kungiyar ‘yan kasuwa a jihar Yobe sun yi addu’o’in samun sauki.

Kungiyar mai suna UMAPO ta gabatar da salla ta musamman don rokan ubangiji ya kawo sauki a halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.