Tsadar Rayuwa: Jigon APC Ya Gaji da Tsarin Tinubu, Ya Nemi a Sake Zama Kan Tsare-tsaren Gwamnati
- Jigon jami'yyar APC a Najeriya, Salihu Lukman ya caccaki jami'yyar yayin da jama'ar kasar ke cikin wani mawuyacin hali
- Salihu ya ce a yanzu kokarin sabunta burin 'yan Najeriya da Tinubu ke yi, ya sabunta kunci ne kawai a rayuwarsu
- Lukman ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a Abuja inda ya bukaci gwamnati ta yi wani abu kan wahalalun da ake ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC a Arewa maso Yamma ya caccaki jami'yyar kan halin da ake ciki.
Salihu Lukman ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a Abuja inda ya bukaci gwamnati ta yi wani abu kan wahalalun da ake ciki.
Mene jigon APC ke cewa kan Tinubu?
Lukman ya ce tsare-tsaren Shugaba Tinubu na sabunta burin 'yan Najeriya ya sabunta musu bakin ciki ne a kasar, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya koka kan yadda tsadar rayuwa ta yi katutu wanda har ya jawo barkewar zanga-zanga a biranen Minna da kuma Kano a ranar Litinin.
Ya kara da cewa wannan duk ya na faruwa ne kasa da shekara daya na mulkin Shugaba Tinubu kan karagar mulkin Najeriya.
Salihu ya bukaci saukin gaggawa a kasar musamman tsadar kayan abinci a kasar da kullum ke tashin gwauron zabi, cewar Independent.
Shawarin Jigon APC ga Tinubu
A cewarsa:
"Akwai munanan labarai daga 'yan Najeriya da ke zuwa kasuwanni wanda farashin ke sauyawa kasa da awanni 24.
"Dukkan wadannan abubuwa na faruwa ne saboda tsare-tsaren da Shugaba Tinubu ke dauka a fannin tattalin arziki.
"Zanga-zangar Minna da Kano ya tabbatar da abin da nake fada a baya cewa akwai matsala idan har ba a dauki matakai ba."
APC ta zargi jam'iyyun adawa kan zanga-zanga
Kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta zargi jam'iyyun adawa da daukar nauyin zanga-zanga da ake yi a kasar.
Jami'yyar ta ce ya kamata sun kawo mafita ne ga matsalar da ake ciki ba wai kushe tsare-tsaren gwamnati ba.
Asali: Legit.ng