Kano: Shugaban Wata Karamar Hukuma a Jihar Ya Yi Murabus, Bayanai Sun Fito
- Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaba karamar hukumar Ungogo a jihar Kano ya yi murabus
- An bayyana cewa Injiniya Abdullahi Ramat ya yi murabus din ne a yau Litinin 5 ga watan Faburairu
- Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Koli
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Shugaban karamar hukumar Ungogo da ke jihar Kano ya yi murabus daga mukaminsa.
Tsohon shugaban karamar hukumar, Injiniya Abdullahi Ramat ya tabbatar da ajiye aikinsa a yau Litinin 5 ga watan Faburairu.
Yaushe Ramat ya yi murabus a kujerar?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin 5 ga watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ramat ya yi godiya ga Ubangiji inda ya ce ya yi iya kokarinsa yayin da ya ke kan kujerar shugabancin karamar hukumar.
Ya ce:
"Alhamdulillah, na mika mulki ga mataimakina, na yi iya abin da zan iya tare sa kaddamar da manyan ayyuka da sunana.
"Na samu kyaututtuka da lambobin yabo ciki da wajen karamar hukumar, na kuma samu lambar yabon ciyaman da ya fi kowa jajircewa daga Majalisar Kano."
Mataimakinsa ya karbi ragamar kujerar mulki
Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni mataimakinsa ya karbi ragamar shugabancin kafin wa'adinsu ya kare.
Hon. Nafi'u Sadiq Yada-Kunya wanda shi ne mataimakin tsohon shugaban karamar hukumar ya karbi ragamar kujerar.
Hon. Nafi'u zai ci gaba da rike kujerar har zuwa karshen wa'adinsu a kan kujerar wanda aka tabbatar bai wuce mako daya daya ba, cewar Radio Kano.
INEC ta sanar da sakamakon zabe a Kano
Kun ji cewa hukumar INEC ta sanar da Bello Muhammad Butu-Butu a matsayin wanda ya lashe zabe a ranar Asabar.
Hukummar ta bayyana cewa Butu-Butu na jam'iyyar NNPP shi ya lashe zaben a mazabar Rimin Gado/Tofa da ke jihar.
Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zaben cike gurbi a fadin kasar baki daya da aka gudanar a ranar Asabar 3 ga watan Faburairu.
Asali: Legit.ng