INEC Ta Sanar da Dan Tsohon Sifetan ’Yan Sanda Wanda Ya Lashe Zaben Majalisa, Bayanai Sun Fito

INEC Ta Sanar da Dan Tsohon Sifetan ’Yan Sanda Wanda Ya Lashe Zaben Majalisa, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da aka kammala gudanar da zaben cike gurbi, hukumar zabe ta fara sanar da sakamoakon zaben a wasu wurare
  • Hukumar ta ayyana Ifeoluwa Ehindero na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar
  • Faresa Johnson Fasinmirin shi ya ayyana Ehindero a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kammala tattara sakamakon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Hukumar zabe ta INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe a mazabar Akoko da ke jihar Ondo a Majalisar Tarayya.

Hukumar ta ayyana Ifeoluwa Ehindero na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Kano: Jami'yyar NNPP ta kifar da APC a zaben cike gurbi a wata mazaba a jihar, bayanai sun fito

INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben Akoko a Ondo
INEC ta sanar da Ehindero na APC wanda ya lashe zaben cike gurbi a Ondo. Hoto: Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Waye INEC ta sanar wanda ya lashe zaben?

Faresa Johnson Fasinmirin shi ya ayyana Ehindero a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kammala tattara sakamakon zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasinmirin ya Ehindero na APC ya samu kuri'u dubu 34,504 yayin da Olalekan Bada na PDP ya samu kuri'u 15,328, cewar Vanguard.

An gudanar da zaben ne don maye gurbin Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo bayan Shugaba Tinubu ya nada shi mukami.

Yawan jam'iyyun da suka fito takara a zaben

Jam'iyyu takwas ne suka tsaya neman takarar kujerar ta Akoko a Majalisar Tarayya da ke jihar Ondo.

Jam'iyyun da suka tsayar da 'yan takara sun hada da APC da PDP da SDP da LP da NNPP da ADC da APGA da kuma APP.

Har ila yau, Hukumar zabe ta sanar da wanda ya yi nasara a zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta bayyana jami'yyar da ta yi nasara a zaben maye gurbin Gbajabiamila, an fadi kuri'u

Hukumar ta bayyana Fuad Laguda na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Surulere a Majalisar Wakilai.

INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe a Kano

Kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi a jihar Kano.

INEC ta fitar da sanarwar ce kan sakamakon zaben cike gurbi a mazabar Rimin Gado/Tofa a Majalisar jihar Kano.

Hukumar ta ayyana Bello Muhammad Butu-Butu na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Rimin Gado/Tofa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.