Sule Lamido Ya Fadi Abu 1 Tak da Zai Iya Fitar Da 'Yan Najeriya Daga Kangin da Suke Ciki
- Babban jigon jam'iyyar PDP, Sule Lamido ya yi tsokaci kan kangin wahalar da 'yan Najeriya ke ciki a yanzu
- Tsohon gwamnan na Jigawa ya bayyana cewa mafita daya da ya ragewa 'yan Najeriya a yanzu shine komawa ga PDP
- A cewar Lamido, gaba daya baragurbin dake cikin PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi kira ga 'yan Najeriya da su gyara kuskuren da suka yi ta hanyar zaben jam'iyyar PDP, ko kuma su ci gaba da zama a halin da suka riski kansu.
A wata hira da ya yi da Arise News a ranar Juma'a, 2 ga watan Fabrairu, Lamido ya kira shawarar a matsayin "zabi tsakanin azzalumai biyu."
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina ganin zabin gab da gab yake. Ko dai ka koma PDP ko ka zauna a kangin wahala. Ka ga duk yadda ka yi nazari, abin da muka sata, duk kazantar mu, sharrinmu bai kai na APC ba.
"Don haka. zabin ’yan Najeriya mugaye ne guda biyu; mugu mai hatsarin gaske wanda shine APC da kuma watakila mugu mai tsafta, wato PDP.
“An zage ni, an wulakanta ni, aka kira ni da mugu. Na shiga bakin ciki iri-iri don kawai na yi kokarin gaya wa ’yan Najeriya labari game da jam’iyyar APC sannan yanzu ga su a mulki kuma suna cewa me."
Gaba daya baragurbin PDP sun koma APC, Lamido
Jigon na PDP ya kuma bayyana cewa baragurbin da suka cike PDP sun koma APC a yanzu, inda suka bar jam’iyyar babu masu son zuciya, rahoton Daily Post.
Lamido ya kuma kara da cewa abin bakin ciki ne yadda wahala ya zama abin da ke hada kan 'yan Najeriya a halin yanzu.
“A koyaushe ina fadin wannan. Najeriya kasa ce mai albarka kuma Allah ya azurta ta da yawan al'umma wanda hakan gagarumin dukiya ne. Amma dai, akwai wani abu da muka rasa.
"A cikin shekaru takwas da gwamnatin APC ta yi, mun sha wahala sannan abin ya ci mana tuwo a kwarya, kuma yanzu an kai mu bango. Yanzu daga mai kudi har talaka duk kuka suke yi.
"A karon farko, mun samu abu guda da ya hada mu wanda shine wahala. Ya kamata a gaggauta yin wani abu. Mun kai karshen hakurinmu; da juriyarmu kuma ba za su iya sake shanye wani abun ba. Ba za mu iya daukar wahala ba."
Masu gaskiya irina ne suka rage a PDP, Sule Lamido
Tsohon gwamnan ya ci gaba da cewa:
"Ya zama dole ka duba dabi'ar mutanen Najeriya. A ganina, dukka baragurbin dake PDP sun fice. Abdullahi Adamu da sauransu sun koma APC, inda suka bar masu gaskiya iri na a PDP.
"Abin da muke da shi yanzu masu gaskiya da 'yan PDP masu tausayi. Yawancin mutanen da ke APC duk 'yan PDP ne kuma sun tafi yanzu sannan abin da muke da shi yanzu masu kyau ne.
"Mutane masu tsarki wadanda suka yarda da Najeriya kuma suke da gaskiya sosai kuma wadanda duk rintsi duk wuya za su tsaya a Najeriya da PDP."
Sule Lamido ya yi raddi ga Akande
A wani labarin, mun ji cewa Sule Lamido ya yi wa Bisi Akande raddi bayan wasu kalamai da ya yi na cewa za a shiga wahala idan PDP ta koma mulki.
Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya zanta da BBC Hausa bayan maganganun da tsohon shugaban rikon kwaryan jam’iyyar APC ya yi.
Asali: Legit.ng