Minista Ya Maida Martani Ga Dattawan da Suka Yi Barazanar Arewa Zata Juyawa Tinubu Baya a 2027

Minista Ya Maida Martani Ga Dattawan da Suka Yi Barazanar Arewa Zata Juyawa Tinubu Baya a 2027

  • Bello Matawalle ya caccaki dattawan jihar Katsina kan barazanar da suka yi na juya wa Tinubu baya a zaɓen 2027
  • Kungiyar dattawan Katsina sun yi barazanar janye goyon bayan Arewa ga Tinubu idan bai sauya tunani kan maida rassan CBN zuwa Legas ba
  • Ƙaramin ministan tsaro ya ce dattawan ba su hurumin yin magana da yawun ɗaukacin al'ummar Arewacin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle, ya maida martani ga ƙungiyar dattawan jihar Katsina kan tazarcen Bola Tinubu a 2027.

Matawalle ya yi fatali da kalaman ƙungiyar, inda ya ce ba ta da hurumin yanke shawara a madadin mutannen Arewa baki ɗaya, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata yayin da ake zargin wani mutumi ya yi ɓatanci ga Annabi SAW a jihar Arewa

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Matawalle: Dattawan Katsina Ba Su da Ikon Magana da Yawun Arewa Kan Zaben 2027 Hoto: Bello Matawalle
Asali: Twitter

Tun farko dai dattawan Katsina sun yi barazanar cewa Arewa za ta juya wa Tinubu baya a zaben 2027 saboda matakin da ya ɗauka na maida wasu sassan CBN zuwa jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Batutuwan da kungiyar dattawan Katsina ta nuna damuwa a kai sun haɗa da sauya wa wasu sassan babban banki wuri tare da hukumar FAAN da aikin faɗaɗa filin jirgin Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.

Dattawan dai kamar yadda rahotanni da dama suka nuna, sun bukaci shugaban kasar da ya janye matakin ko kuma ya rasa goyon bayan yankin Arewa a zaben 2027.

Matawalle ya maida martani ga dattawan Katsina

Yayin da yake shirin tafiya kasar Saudiyya domin halartar taron ministocin tsaro na duniya a birnin Riyadh da yin Umrah, Matawalle ya ce barazanar da Dattawan Katsina suka yi ba komai ba ce.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mutane 30 sun mutu yayin da wani abu ya fashe a jihar APC, bayanai sun fito

Tsohon gwamnan Zamfaran ya ce wannan barazanar za ta iya haifar da ƙiyayya, rashin haɗin kai da sa ƴan Arewa su tsani ƴan uwansu na sauran sassan Najeriya.

Ya ce ba daidai ba ne dattawan su yi irin wannan gurɓatacciyar magana ta barna a madadin Arewacin Najeriya alhali sun san ba shi ne ra’ayin jama’ar yankin ba, rahoton Daily Post.

Matawalle ya bayyana cewa shugaba Tinubu na dukkan ‘yan Najeriya ne kuma ba shi da wata manufa ko ajanda ta yaƙar ko ɗaya daga cikin shiyyoyi shida na kasar nan.

“Saboda haka, ina shawartan dattawan Katsina su sauya tunani, su daina ɗaukar siyasa da zafi, su mayar da hankali kan abin da zai dunƙule ‘yan Nijeriya da ƙasa domin ci gaba," in ji shi.

IG ya bada umarnin taƙaita zirga-zirga

A wani rahoton kun ji cewa IGP Kayode ya bada umarnin taƙaita zirga-zirgan ababen hawa a jihohi 26 da za a yi zaben cike gurbi ranar Asabar.

Shugaban rundunar ƴan sandan ya hana zirga-zirga daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa 6:00 na safe a waɗannan jihohi da suka kunshi Legas da Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262