Watanni Kadan Bayan Mutuwar Shugabar Matan PDP, an Maye Gurbinta da Amina, Bayanai Sun Fito
- Jam'iyyar PDP ta nada sabuwar shugabar matan jam'iyyar bayan mutuwar wacce ta rike mukamin a baya
- Jam'iyyar ta PDP a Najeriya ta amince da nadin Hon. Amina Divine a matsayin shugabar mata na jam'iyyar
- Wannan nadin na zuwa ne bayan mutuwar shugabar matan, Farfesa Stella Effah-Attoe a watan Oktobar 2023
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta amince da nadin Hon. Amina Arong Divine a matsayin shugabar mata na jam'iyyar.
Amina Arong ta shahara wurin hada kan mata a Najeriya ga jam'iyyar don samar da ci gaba.
Yaushe aka nada Amina shugabar matan PDP?
Wannan nadin na zuwa ne bayan mutuwar shugabar matan, Farfesa Stella Effah-Attoe a watan Oktobar 2023, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren yada labaran jam'iyyar, Debo Ologunagba shi ya sanar da haka a shafin X a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu.
Arong wacce ta fito daga jihar Cross Rivers ta karanci bangaren kudade da aikin banki da kuma kididdigar kudade.
Sabuwar shugabar matan za ta ba da gudunmawa sosai da ci gaban jam'iyyar ganin irin yadda ta ke da kwarewa.
Wane shawari jam'iyyar ta ba ta?
Jam'iyyar ta bayyana cewa ta nada Amina ce ganin irin kokarin da ta ke yi wurin hada kan mata a jam'iyyar.
Ta kuma ce Hon. Amina ta ba da gudunmawa wurin tabbatar da gudanar zabukan fidda gwani na jam'iyyar a matakai da dama.
Jam'iyyar ta taya Amina murna inda ta bukace ta da ta yi amfani da kwarewar da ta ke dashi don ciyar da jam'iyyar gaba.
Ta shawrce ta da ta yi hadaka da sauran kwamitocin jam'iyyar don samun hadin kai da ci gaban jam'iyyar a ko wane bangare.
Jigon jam'iyyar PDP ta riga mu gidan gaskiya
Kun ji cewa Jam’iyyar PDP ta shiga cikin jimami bayan mutuwar shugabar mata ta jam’iyyar, Farfesa Stella Effan-Attoe.
Jam’iyyar ta ce wannan rashi ba iya jam’iyyar PDP kawai ba ne, har ma da sauran ‘yan Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng