Shekarau Ya Fadi Kuskuren Ganduje a Gayyatar da Ya Yi Wa Gwamna Abba Ta Shiga APC
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau bai gamsu da gayyatar da Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Gwamna Abba ta shiga APC ba
- Tsohon sanatan ya bayyyana cewa matakin da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya ɗauƙa abu ne wanda bai kamata
- Shekarau ya yi nuni da cewa kamata ya yi Ganduje ya yi kira ga al'ummar jihar Kano da su zauna lafiya da junansu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya yi magana kan gayyatar da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa Gwamna Abba Kabir ta komawa APC.
Shekarau wanda tsohon sanata ne ya bayyana gayyatar a matsayin matakin da bai kamata ba.
Jaridar Daily Trust ta ce Shekarau wanda ya taɓa zama gwamnan jihar har na wa’adi biyu wanda tsohon ministan ilimi ne ya bayyana hakan ne a wani saƙon bidiyo da ya aike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Kano, ya je Kano domin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a makon da ya gabata, inda ya miƙa gayyata ga Gwamna Abba da sauran ƴan jam’iyyar NNPP da su shigo APC.
Wane martani Shekarau ya yi?
Da yake mayar da martani kan gayyatar, Shekarau ya bayyana cewa:
"Ɗan uwana Ganduje ya zo Kano ya gayyaci Gwamna Abba, Rabiu (Kwankwaso) da sauransu su zo su shiga APC. A gani na, wannan bai kamata ba.
"Abin da ya kamata ya yi shi ne ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su zauna lafiya ba tare da la’akari da wanda ke shugabantarsu ba, tunda an gama shari’ar.
"Ko ka zage su ko ba ka zage su ba, ko sun san yadda za a yi ko ba su sani ba, su ne ke kan mulki."
Uzodinma Ya Tura Saƙo Ga Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma, ya tura saƙo ga Gwamna Abba kan batun komawa APC.
Uzodinma ya yi nuni da cewa za su yi maraba da gwamnan cikin jam'iyyar APC saboda muhimmancin da Kano take da shi a siyasance.
Asali: Legit.ng