Shin da Gaske Yahaya Bello Na Neman Kujerar Ganduje? Gaskiya Ta Bayyana

Shin da Gaske Yahaya Bello Na Neman Kujerar Ganduje? Gaskiya Ta Bayyana

  • Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya fito ya yi magana kan batun neman shugabancin jam'iyyar APC
  • Yahaya Bello ya yi nuni da cewa sam babu hannunsa a fastocin da ake yaɗa wa masu muna cewa yana neman shugabancin APC
  • Tsohon gwamnan na Kogi ya buƙaci jama'a da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗa wa kan cewa yana neman kujerar Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya nesanta kansa da hotunan da ke alaƙanta shi da neman muƙamin shugaban jam’iyyar APC.

Wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na tsohon gwamnan ya fitar a ranar Talata ta dora alhakin yaɗa hotunan nasa a kan "wasu shugabannin ƴan adawa da wasu masu bita da ƙulli a jam'iyyar.", cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jam'iyyar APC ta yi magana kan tsohon gwamnan arewa da ke son tsige Ganduje

Yahaya Bello ya magantu kan neman kujerar Ganduje a APC
Yahaya Bello ya musanta neman shugabancin jam'iyyar APC Hoto: @OfficialGYBKogi, @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Ofishin yada labarai na tsohon gwamnan ya lura cewa ana yin hakan ne da nufin ɓata sunan tsohon gwamnan, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Yahaya Bello ya ce kan takararsa?

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Wasu daga cikin tsare-tsare da tuni aka fara shiryawa akwai yaɗa fastoci ɗauke da hoton mai girma Alh. Yahaya Bello, CON, tsohon gwamnan jihar Kogi, masu nuna cewa yana neman kujerar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa. Jitar-jitar ƙarya ce kuma kuma ya kamata a yi watsi da ita.
"Jam’iyyarmu ba ta cikin tsarin gudanar da taro ko babban taro na ƙasa, don haka babu wani dalili da zai sa wani ya riƙa yaɗa duk wata fosta ta ofisoshin jam’iyya.
"Bari a fayyace cewa mai girma Alhaji Yahaya Bello bai baiwa kowa izinin yaɗa wata fosta a madadinsa ba domin ya kasance mai biyayya ga jam’iyya, mai kishin jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, mai girma Dr Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

Shettima ya bayyana gaskiya kan shirin gwamnatin Tinubu na mayar da manyan ofisoshi zuwa Legas

"Muna kira ga jama'a da su yi watsi da mutanen da ke yaɗa fastocin don haifar da labari na ƙarya."

APC Ta Yi Martani Kan Takarar Yahaya

A wani labarin ka, kun ji cewa, jam'iyyar APC ta yi martani kan neman shugabancinta da aka.ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, na yi.

Jam'iyyar ta yi nuni da cewa babu sauran gurbi a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa wanda Yahaya Bello zai cike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng