Bayan Sha Da Kyar A Kotun Koli, Gwamnan Arewa Ya Dage Zaben Ciyamomi Kan Dalili 1, Bayanai Sun Fito

Bayan Sha Da Kyar A Kotun Koli, Gwamnan Arewa Ya Dage Zaben Ciyamomi Kan Dalili 1, Bayanai Sun Fito

  • Bayan Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya yi nasara a kotu, hukumar zaben jihar ta dage gudanar da zaben ciyamomi
  • Hukumar ta NASIEC ta ce ta dage gudanar da zaben ne saboda shari'ar da ake bayan wasu sun aike musu sammaci da Majalisar jihar
  • Shugaban hukumar, Barista Ayuba Usman Wandai shi ya bayyana haka a jiya Litinin 29 ga watan Janairu yayin ganawa da IPAC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa - Hukumar zaben jihar Nasarawa (NASIEC) ta dage gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.

Idan ba a mantaba, NASIEC ta shirya gudanar da zaben ne a ranar 31 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Jama'a sun shiga tashin hankali gobara ta kame wasu makarantun sakandare a Anambra

Nasarawa ta dage zaben ciyamomin kananan hukumomi kan wasu dalilai
Hukumar zabe a Nasarawa ta dage zaben kananan hukumomi. Hoto: Abdulllahi Sule.
Asali: Facebook

Mene dalilan dage zaben a Nasarawa?

Sai dai hukumar ta sanar da dakatar da shirin gudanar da zaben har sai baba ya gani saboda wasu matsaloli, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar, Barista Ayuba Usman Wandai shi ya bayyana haka a jiya Litinin 29 ga watan Janairu yayin ganawa da mambobin IPAC.

Wandai ya ce babban dalilin dage shirin gudanar da zaben bai rasa nasaba da yawan sha'anin shari'a da ta dabaibaye shirye-shiryen.

Ya ce sun dauki matakin ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Lafia ta aike musu da sammaci da wasu ke kalubalantar Majalisar jihar da hukumar.

Matakin da hukumar zaben ta dauka

Ayuba ya ce ganin haka ya saka hukumar fahimtar hakan zai kawo mata cikas a gudanar da zaben wanda ya tilasta su daukar wannan mataki.

Wandai ya ce sun bukaci lauyoyinsu da saka himma wurin tabbatar da fara shari'ar don basu damar fara shirye-shiryen zaben, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki ya sake faruwa a Ibadan yayin da gobara ta tashi a ofishin INEC, an yi karin bayani

Ya ce:

"Duba da abubuwan da muka lissafo a sama, hukumar ta yanke shawarar dage zaben da aka tsara a ranar 31 ga watan Agusta har sai baba ya gani."

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Sule

Kun ji cewa, Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Har ila yau, kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, David Ombugadu saboda rashin gamsassun hujjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.