Gwamnan APC, Tsoffin Gwamnoni 2 da Wasu Manyan Ƙusoshi Sun Dira Kotun Koli Ana Shirin Yanke Hukunci

Gwamnan APC, Tsoffin Gwamnoni 2 da Wasu Manyan Ƙusoshi Sun Dira Kotun Koli Ana Shirin Yanke Hukunci

  • Gwamnan Nasarawa da wasu manyan jiga-jigan siyasa sun mamaye Kotun Koli yayin da ta shirya yanke hukunci kan karrraki da dama yau Jumu'a
  • Abdullahi Sule da tsoffin gwamnoni 2 da suka gabace shi a Nasarawa yanzu haka sun nemi wuri sun zauna a harabar kotun
  • Shari'ar zaben gwamnan Nasarawa na ɗaya daga cikin waɗanda kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya za ta ƙarƙare a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, da magabantansa guda biyu sun isa Kotun Ƙolin Najeriya yayin da ta tsara yanke hukunci kan nasarar Sule a 2023.

Gwamna Sule da tsoffin gwamnonin guda biyu na cikin manyan jiga-jigan siyasar da aka gani sun nemi wuri sun zauna a kotun yayin da ake dakon hukuncin ƙarshe.

Kara karanta wannan

Isah Vs Uba Sani: Kotun Koli ta bayyyana sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan Kaduna

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
Gwamma Sule, Tsoffin Gwamnoni 2 da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Kotun Koli Hoto: Abdullahi Sule
Asali: Twitter

Tsofaffin gwamnonin jihar Nasarawa da suka halarci zaman kotun kolin sune, Abdullahi Adamu da Umar Tanko Al-Makura, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun Ƙoli ta sanya yau Jumu'a, 19 ga watan Janairu, 2024 domin yanke hukunci kan ƙararraki huɗu da ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP, Emmanuel David Ombugadu, ya shigar.

Daga cikin rokon da ya yi a ƙarar da ya ɗaukaka zuwa gaban Kotun Ƙoli, Ombugadu ya nemi a rushe nasarar Gwamna Sule, ɗan takarar gwamna a inuwar APC.

Gwamnoni 9 zasu san makomarsu yau

Rahoton Vanguard ya nuna cewa Kotun Ƙolin ta tsara yanke hukunci kan taƙaddamar zaben gwamnonin jihohi 9 ranar Jumu'a, 19 ga watan Janairu, 2024.

Jihohin da kotun kolin ta saurari kararrakin da aka shigar gabanta kuma ta tanadi hukunci sune Delta, Ribas, Kebbi, Nasarawa, Taraba, Sokoto, Gombe, Kaduna da Ogun.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta raba gardama, ta faɗi asalin wanda ya lashen zaɓen gwamna a jihar arewa

Yayin da mai shari’a Inyang Okoro zai jagoranci kwamitin da zai yanke hukunci kan wasu kararrakin, ɗayan kwamitin kuma ƙarkashin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun zata yanke sauran.

Gwamnan Yahaya ya yi nasara a ƙarara ADC

A wani rahoton kuma Ƙoli ta yanke hukunci kan karar da jam'iyyar ADC da ɗan takarar gwamna suka nemi tsige Gwamna Inuwa Yahaya.

A zaman sauraron karar, kotun ta yi watsi da ƙarar bayan lauyan masu kara ya janye, ta kuma sanya ranar yanke hukunci a ƙarar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel