A Karshe, Gwamna Abba Kabir Ya Yi Martani Kan Yarjejeniyarsu da Tinubu Don Komawa APC, Ya Yi Godiya
- A karshe, Gwamna Abba Kabir ya yi martani kan jita-jitar da ake yi cewa akwai yarjejeniya tsakaninsa da Tinubu
- Abba ya karyata kulla yarjejeniya cewa zai koma APC da kuma maganar masarautu da dakatar da rusau
- Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ya bayyana haka inda ya ce babu kamshin gaskiya a takardun da ke yawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi martani game da jita-jitar yarjejeniya da jam’iyyar APC.
Abba Kabir ya musanta kulla wata yarjejeniya da Shugaba Tinubu kafin yanke hukuncin Kotun Koli a ranar 12 ga watan Janairu.
Wane martani Abba Kabir ya yi?
Yayin da ya ke martani kan wasu takardu da ke yawo a kafafen sadarwa, kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi fatali da hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bature ya ce kawai an kirkire su ne don cimma wani buri amma babu kamshin gaskiya ko kadan tattare da takardun.
Har ila yau, Sanusi ya karyata cewa a cikin yarjejeniyar wai akwai dakatar da rusau da kuma maganar masaurautu da aka kirkira, cewar Leadership.
A cewarsa:
“Don karin bayani kan jita-jitar yarjejejniya da gwamna cewa zai koma APC da maganar masarautu da kuma dakatar da rusau.
“Gwamnan ya na son fayyace komai cewa bayan yin nasara a zabe da kuma tabbatar da shi a kotu ba ya tsoron wata barazana daga ‘yan sha miyar siyasa.
“Sannan su sani su masu fakewa a rigar shugaban kasa cewa dukkan wani mataki da za a dauka za a yi ne ta hanyar da ta dace karkashin ikon mai girma gwamna.”
Gwamnan ya yi godiya ga Tinubu
Gwamnan har ila yau, ya godewa Shugaba Tinubu da kokarinsa wurin tabbatar da barin shari'a ta yi aikinta yayin hukuncin.
Sannan ya ce babu wani abu da zai hana shi ayyukan aikairi kamar yadda ya ke yi da zai inganta al’ummar jihar Kano, cewar SolaceBase.
Ya kara da cewa:
“Mun musanta jita-jitar cewa akwai wata yarjejeniya da Tinubu sai dai mu gode masa kan nuna girma yayin shari’ar da aka yi.
“Tabbas yadda ya ki amincewa da biye wa wasu jiga-jigan jam’iyyarsa abin yabawa ne daga al’ummar jihar Kano.”
Tinubu zai kara albashi
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya shirya karin mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar.
Tinubu ya kafa kwamiti da za su yi zauna don tabbatar da aiwatar da mafi karancin albashin.
Asali: Legit.ng