Na Hannun Daman Atiku Ya Sake Sanya Labule da Tinubu a Paris, Bayanai Sun Fito

Na Hannun Daman Atiku Ya Sake Sanya Labule da Tinubu a Paris, Bayanai Sun Fito

  • Shugaba Bola Tinubu ya gana da tsohon kakakin Atiku Abubakar, Daniel Bwala, a karo na biyu a kasar Faransa
  • Bwala, jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana ganawarsa da shugaban ƙasar a karo na biyu cikin makonni biyu a ranar Litinin a shafinsa na X
  • Jigon na PDP ya bayyana cewa, shugaba Tinubu ya bayyana masa ra’ayinsa game da ceto Najeriya a ganawar da suka yi a birnin Paris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Paris, Faransa - Daniel Bwala, tsohon mai magana da yawun ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a birnin Paris.

Bwala wanda babban lauya ne ya sanya labule da shugaban ƙasar ne a ranar Litinin, 29 ga watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kano: Ganduje ya tura sako mai muhimmanci game da alakarsa da su Kwankwaso

Bwala ya sa labule da Tinubu
Daniel Bwala ya sanya labule da Shugaba Tinubu Hoto: @BwalaDaniel
Asali: Twitter

Daniel Bwala ya ziyarci Tinubu a Aso Rock

Ku tuna cewa jigon na PDP ya gana da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa makonni biyu da suka gabata, inda ya ce lokaci ya yi da za a mara wa gwamnati mai ci baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ziyarar da ya kai fadar Villa, lauyan ya ce ya zo ne bisa gayyatar da Shugaba Tinubu ya yi masa, inda ya bayyana shi a matsayin uban ƙasa.

Bwala ya ci gaba da cewa Allah ya ba da damar jagorantar ƴan Najeriya zuwa ga Tinubu, kuma ya kai ziyara ne domin murna da taya shugaban ƙasar murna.

Ya kuma bayyana wa shugaban ƙasa ƙudirinsa na marawa gwamnatin Tinubu baya, inda ya ƙara da cewa lokaci ya yi da ƴan adawa za su mara wa sabuwar gwamnati baya.

Bwala, Tinubu Sun Haɗu a Paris

Kara karanta wannan

Babban minista ya fadi abu 1 da yake hana Shugaba Tinubu barci

Jigon na jam'iyyar PDP a ranar Litinin ya wallafa haɗuwarsa karo na biyu da Tinubu a shafinsa na X.

Ya rubuta cewa:

"Abin farin ciki ne na gana da uban ƙasa @officialABAT shugaban kasa Bola Tinubu a birnin Paris a yau. Ya ci gaba da bayyana ra’ayinsa tare da nuna sha’awarsa na jagorantar Najeriya zuwa ga tudun mun tsira."

Bwala Ya Magantu Kan Yiwuwar Samun Muƙami Wajen Tinubu

A baya rahoto ya zo cewa Daniel Bwala ya yi magana kan yiwuwar samun muƙami a gwamnatin Shugaba Tinubu.

Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa idan Tinubu ya ba shi muƙami, zai karɓa domin yin aiki a gwamnatinsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng