An Zo Wajen: Kotun Koli Ta Dauki Mataki Kan ‘Karar Binani da Ta Nemi Tsige Gwamnan Adamawa

An Zo Wajen: Kotun Koli Ta Dauki Mataki Kan ‘Karar Binani da Ta Nemi Tsige Gwamnan Adamawa

  • Kotun Koli ta tanadi hukunci a karar da jam'iyyar APC da 'yar takararta, Aisha Binani suka daukaka na neman a soke zaben Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa
  • Bayan lauyoyin bangarorin sun yi muhawararsu ta karshe, Kotun Kolin ta sanar da cewar ta tanadi hukunci sannan cewa za a sanar da jam'iyyun idan an tsayar da rana
  • Ku tuna cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Gwamna Fintiri na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Adamawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Yola, Jihar Adamawa - Kotun Koli ta jingine hukunci a 'karar da jam'iyyar APC da 'yar takararta na zaben gwamna a jihar Adamawa, Aisha Dahiru Binani suka daukaka kan gwamnan jihar, Ahmadu Fintitri.

Kara karanta wannan

Landan: An kwantar da Sarki Charles a asibiti, cikakken bayanai sun fito

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, kwamitin mutum biyar na Kotun Kolin karkashin jagorancin John Okoro ne suka dauki matakin a ranar Litinin, 29 ga watan Janairu.

Kotun Koli ta tanadi hukunci a shari'ar Aisha Binani
An Zo Wajen: Kotun Koli Ta Sa Ranar Yanke Hukunci a ‘Karar Binani da Ta Nemi Tsige Gwamnan Adamawa Hoto: @realaishabinani, @GovernorAUF
Asali: Twitter

Kwamitin Okoro ya dage zaman don yanke hukuncin karshe, bayan sauraron muhawara daga bangarorin da abun ya shafa, rahoton Blueprint.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani hukunci kotunan kasa suka yanke?

Da farko dai kotun sauraron 'kararrakin zabe na jihar da kotun daukaka kara sun yi watsi da 'karar da Binani ta shigar, tana kalubalantar nasarar Fintiri a zaben gwamnan da aka yi a jihar.

Kotun daukaka karar dai ta tabbatar da nasarar Fintiri na jami'yyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.

Kotun ta kuma yi fatali da korafe-korafen Hajiya Aisha Binani ta jami'yyar APC saboda rashin gamsassun hujjoji, a ranar Litinin, 18 ga watan Disambar 2023.

Kara karanta wannan

Rashawar $500,000: Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan zaman Farouk a gidan yari na shekara 5

Daga cikin hujjojin da kotun ta bayar shi ne rashin kawo shaidu kamar malaman zabe da su ke rumfunan zabe da aka gudanar.

Kotun Koli ta yanke hukunci a zaben Ribas

A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Rivers.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Siminalayi Fubara na PDP a matsayin halattaccen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng