Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Na Karshe Kan Shari’ar Neman Tsige Gwamnan PDP a Jihar Arewa

Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Na Karshe Kan Shari’ar Neman Tsige Gwamnan PDP a Jihar Arewa

  • Mai shari'ar Okoro, shugaban kwamitin mutum biyar na Kotun Koli ya yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Adawa
  • A hukuncin da ya yanke, Okoro ya ce duka masu shigar da karar sun gaza gabatar da kwararan hujjoji da za su tabbatar da zarge-zargen su
  • Dan takarar jam'iyyar SDP, Dr Umar Ardo ne ya shigar da kara a Kotun Koli don kalubalantar nasarar Gwamna Fintiri a zaben jihar na 2023

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Laraba ne kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP, Dr Umar Ardo, ya shigar kan zaben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Ana daf da yanke hukunci a Kano, Ganduje ya nemi alfarma daga 'yan adawa a jihar arewa

Ardo ya garzaya Kotun Koli yana neman a yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa da na Kotun Daukaka Kara suka yanke kan shari'ar zaben.

Kotun ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
Kotun Koli ta yanke hukunci na karshe kan shari'ar neman tsige Gwamna Fintiri na jihar Adamawa. Hoto: @GovernorAUF
Asali: Twitter

Wanda ya shigar da kara ya bukaci kotun ta soke zaben da ya samar da Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa saboda rashin bin dokar zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yanke hukunci bayan masu kara sun janye

A nasa bangaren, Mai shari’a Okoro, ya shaida wa lauyan cewa hujjojin da suka gabatar sun nuna cewa karar da suka shigar ba ta da inganci, Tribune Online ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito Lauyan mai karar Mr Imahnobe ya nemi a janye karar, bukatar da wadanda ake kara ba su yi adawa da ita ba.

Don haka, Mai shari’a Okoro ya yi watsi da karar kuma ya ce “sauran masu karar za su bi wannan sakamakon da kotun ta yanke”.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar karshe ta neman tsige gwamnan PDP, ta ba da bahasi

Tun da farko Kotun Daukaka Kara, a hukuncin da mai shari’a Ugochukwu Ogaku ya yanke, ta ce wadanda suka shigar da karar ba su kawo hujjojin da suka tabbatar da da almundahana da rashin bin dokar zabe da suke zargin hukumar INEC ta yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel