Jigon APC Ya Fadi Dalili 2 da Ya Kamata Ya Sanya a Bari Sulhun Kwankwaso da Ganduje Ya Yi Aiki

Jigon APC Ya Fadi Dalili 2 da Ya Kamata Ya Sanya a Bari Sulhun Kwankwaso da Ganduje Ya Yi Aiki

  • Bashir Ahmad na jam’iyyar APC ya ce ya kamata ƴan siyasa a Kano su yi watsi da bukatunsu na ƙashin kai
  • Ahmad ya ce ya kamata ƴan siyasa a jihar su kiyaye maganganunsu, kuma su bar sulhun da shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar ya yi aiki
  • Tsohon hadimin shugaban ƙasar ya bayyana cewa idan sulhun ya yi aiki, zai kasance mai mahimmanci saboda wasu dalilai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kano, jihar Kano - Bashir Ahmad, tsohon mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa na zamani ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya roƙi ƴan siyasa a jihar Kano da su yi watsi da buƙatunsu na ƙashin kansu a yanzu.

Ahmad a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ya kamata mambobin jam’iyyar NNPP da jam’iyyar APC su ƙyale sulhu ya yi aiki.

Kara karanta wannan

Babban minista ya fadi abu 1 da yake hana Shugaba Tinubu barci

Bashir ya magantu kan sulhun Ganduje da Kwankwaso
Bashir Ahmad ya ce sulhun Kwankwaso da Ganduje alheri ne ga Kano Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Abar sulhun Kwankwaso, Ganduje ya yi aiki’ - Ahmad

Ku tuna cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya fara yunƙurin sulhunta jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso da kuma shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu majiyoyi da dama sun ce shugaban ya bayyana aniyarsa ga mutanen biyu daban-daban kuma ya ba su wani lokaci domin su sanar da masu ruwa da tsaki kan aniyarsa sannan su dawo nan gaba kaɗan domin kammala sulhun.

Da yake mayar da martani, Bashir ya tabbatar da cewa APC da jihar Kano "suna bukatar sulhun". Ya ce ana buƙatar sulhun ne saboda wasu muhimman dalilai.

Na farko a cewarsa bukatar ci gaban jihar Kano. Dalili na biyu kuma a cewarsa shi ne don haɗin kai.

Bashir Ahmad ya rubuta a shafinsa na Twitter a yammacin ranar Asabar, 27 ga watan Janairu cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana abu 1 da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a jiharsa

"Don Allah ƴan siyasa a Kano su ajiye buƙatunsu na ƙashin kansu a yanzu, su kiyaye maganganunsu, a bar sulhu ya yi aiki, muna buƙatarsa.
"Wannan sulhu yana da matuƙar muhimmanci saboda dalilai guda biyu: don tabbatar da ci gaban jiharmu ba tare da cikas ba da kuma tabbatar da haɗin kan al'ummarmu."

Ganduje Ya Buƙaci Gwamna Abba Ya Dawo APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya dawo APC.

Ganduje ya yi wannan kiran ne a wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da aka gudanar a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng