Kano: Ganduje Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Kwankwaso Ya Koma Jam'iyyar APC Su Sake Haɗuwa

Kano: Ganduje Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Kwankwaso Ya Koma Jam'iyyar APC Su Sake Haɗuwa

  • Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan masu tunanin alaƙarsa da Kwankwaso ba zata yi ƙarko ba ko sun haɗu a APC
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce yana da ƙwarin guiwar zasu sake haɗewa wuri ɗaya domin tun usuli a tare aka gansu
  • Ya kuma kara tabbatar da cewa sun aike da goron gayyatar shiga APC ga Kwankwaso da Abba Gida-Gida

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana kwarin guiwar cewa zasu sake zama inuwa ɗaya da Rabiu Kwankwaso, jagoran NNPP na ƙasa.

Duk da tsawon lokacin da suka shafe suna zaman doya da manja, Ganduje ya ce ba abin mamaki bane shi da tsohon gwamnan su sake cure wa wuri ɗaya domin dama tare suke.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya maida martani ga Ganduje kan roƙon sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC

Dakta Abdullahi Ganduje da Kwankwaso.
Kano: Ina da yakinin alakata da Kwankwaso za ta yi kyau – Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, KwankwasoRM
Asali: Twitter

A wata hira da BBC Hausa, Ganduje ya ce tuni suka aike da goron gayyata zuwa ga Abba Kabir Yusuf, gwamnan Kano da kuma jagoran NNPP na ƙasa, Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, Ganduje ya ce:

"Wannan ya zama tilas saboda a matsayina na shugaban APC na ƙasa, na fara zagayawa jihohi, kuma na ga yadda sanatoci da ƴan majalisar wakilan tarayya suke shigowa jam'iyyar mu, har ma da gwamnoni.
"Na kira mutane da dama a sassan kasar nan ballantana waɗanda ke nan a jihata."

Shin APC ta aike da wasiƙar gayyata ga Kwankwaso da Abba?

Dangane da batun aika sakon gayyatar shiga APC a hukumance, tsohon gwamnan ya ce har yanzun ba su aika da wasiƙa a hukumance ga Kwankwaso da Abba ba.

Sai dai ya ce suna son sai lokacin da tsagin Kwankwaso da magoya bayansa ƴan Kwankwasiyya suka nuna sha'awar shiga APC sannan zasu rubuta masu wasiƙa.

Kara karanta wannan

"Yan ta'adda sun lalata kaso 90 cikin 100 na gidajen al'ummar jihata" Gwamna ya faɗi gaskiya

Da yake ƙarin haske kan shakkun jama'a cewa ba abu ne mai yiwuwa manyan ƴan siyasan su iya zama a inuwa ɗaya ba, Ganduje ya ce dama tun asali su ƴan gida ɗaya ne.

Daily Trust ta rahoto Ganduje na cewa:

"Dama tun usuli gidan mu ɗaya, uwa ɗaya uba ɗaya, matsala ta faru aka rabu amma yanzu idan Allah ya sake haɗawa, abun zai yi kyau."

Gwamna Abba ya aike da saƙo ga Ganduje

A wani rahoton kuma Gwamna Abba na Kano ya mayar da martani kan kokon barar da Ganduje ya aike masa na ya bar NNPP ya koma jam'iyyar APC.

A wurin taron masu ruwa da tsaki, Ganduje ya roki gwamnan Kano da NNPP su aje komai a gefe, su taho zuwa APC mai mulkin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262