Tsohon Gwamna Ya Gargadi Ganduje a Kan Kuskuren da Zai Iya Sake Rusa Jam’iyyar APC
- Oserhemen A. Osunbor ya shiga neman takarar gwamna a jihar Edo a karkashin jam’iyyar APC
- Farfesan ya rasa kujerar gwamnan ne shekaru 16 bayan hukuncin kotun kolin da ya ba AC mulki a Edo
- Osunbor ya bukaci shugabannin APC na kasa su shirya zaben tsaida ‘dan takara na gaskiya da adalci
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Oserhemen A. Osunbor ya bukaci adalci daga majalisar NWC ta jam’iyyar APC wajen tsaida ‘dan takaran gwamnan Edo.
A shekarar 2024 za a shirya zaben sabon gwamna a Edo, Daily Trust tace Oserhemen A. Osunbor yana cikin masu neman mulki.
Farfesa Oserhemen A. Osunbor ya yanki fam, inda bayan nan ya kira ga jam’iyyar APC ta guji maimaita kuskuren da aka yi a 2020.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya nuna laifin shugabannin jam’iyya ne ya jawo APC ta rasa mulkin jihar Edo a zaben da aka yi wancan karo.
Sabanin gwamna Godwin Obaseki da tsohon mai gidansa, Adams Oshiomhole ya yi sanadiyyar da gwamnati ta bar hannun APC.
Oserhemen A. Osunbor ya saye fam a APC
Da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyya mai mulki da ke birnin Abuja, Farfesa Osunbor ya roki ayi wa kowa adalci.
Farfesan yana so shugabannin jam’iyya a karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje su shirya zaben tsaida gwani na adalci.
Idan aka yi gaskiya ba tare da amfani da tasirin manya ba, tsohon gwaman yana ganin za a samu zaman lafiya a iya lashe zabe.
APC: Tsohon gwamna zai yi takara
A shekaru 72, Punch ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa bai tsufa da zama gwamnan jihar Edo ba, yana sa ran ya gaji Godwin Obaseki.
Oserhemen Osunbor wanda ya yi Sanata sau biyu ya saye fam a kan N50m domin ya koma kujerar da ya rasa tun a shekarar 2008.
Idan ya koma mulki, ya yi alkawarin samar da abubuwan more rayuwa, ya kuma ce bai da wata matsala da Adams Oshiomhole.
An zargi Ganduje da kashe APC
An ji labari Mai ba gwamnan Kano shawara, Anas Dala yayi kaca-kaca da Abdullahi Ganduje, ya zarge shi da kashe jam'iyyar APC.
‘Dan siyasar ya yi maganar kiran da ake yi na dunkulewa tsakanin NNPP da jam’iyya mai rike da kasa bayan hukuncin kotun koli.
Asali: Legit.ng