Zaben Edo: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Gwamna Obaseki

Zaben Edo: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Gwamna Obaseki

- Gwamna Godwin Nogheghase Obaseki wanda ya kasance dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan Edo ya lashe zabe a karo na biyu

- An haifi Obaseki a ranar 1 ga watan Yuli, 1959 a Benin City

- Kafin zamowarsa gwamna, Obaseki ya shugabanci kamfanoni da dama

Gwamna Godwin Nogheghase Obaseki wanda ya kasance dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a jiya Asabar, 19 ga watan Satumba ya yi nasarar lashe zaben.

KU KARANTA KUMA: Sakamakon zaben Ƙananan hukumomi 16: Obaseki ya zarce Ize-Iyamu da ƙuri'u 87,677

Zaben Edo: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Gwamna Obaseki
Zaben Edo: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Gwamna Obaseki
Asali: Original

1. Haihuwarsa

An haifi Obaseki a ranar 1 ga watan Yuli, 1959 a Benin City, Nijeriya. Obaseki ne da na uku a wajen mahaifansa.

2. Tarihin karatunsa

Ya yi karatunsa na firamare a makarantar St. Matthew daga nan ya tafi makaratar Eghosa Grammar School, a Birnin Benin, inda ya yi karatunsa na sakandare.

Daga nan Obaseki ya tafi makarantar jami’a na Ibadan, inda ya samu kwalinsa na digiri. Ya kuma yi bautar kasa a garin Jos, babbar birnin jihar Plateau.

Bayan nan sai ya tafi kasar Amurka inda yayi karatun gaba da digiri a fannin kudi da kasuwanci.

3. Tarihin aikinsa

Obaseki ya fara aiki da kamfanin Capital Trust Brokers Limited, Lagos a 1983 daga nan aka mayar dashi zuwa the International Merchant Bank.

Bayan nan ya koma AVC Funds Limited, Lagos, a 1988, inda yayi aiki a matsayin Manaja. Daga nan sai ya koma birnin New York a matsayin shugaban wani kamfanin bada shawarwari kan kudi.

Obaseki ya rike shugabancin manyan kamfanoni masu zaman kansu, kamar su Afrinvest.

4. Bangaren Siyasa

Ya kasance shine Shugaban tawagar tsare-tsaren tattalin arziki ta Jihar Edo, wanda tsohon gwamna Adams Oshiomole ya kaddamar a watan Maris ta 2009.

Obaseki ya zama gwamnan jihar Edo karkashin jam’iyyar APC a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2016.

Godwin Obaseki ya sauya sheka daga Jam’iyyarsa ta APC zuwa PDP kwanaki bayan hana shi sake takarar da aka yi.

KU KARANTA KUMA: Hankalinmu ba zai kwanta ba har sai an fadi sakamakon zaben kananan hukumomi 2 - PDP

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar jami’ansa da magoya bayansu zuwa Cibiyar Jam’iyyar PDP da ke Benin inda aka karbe shi hanu bibiyu.

Rikici tsakanin Obaseki da ubangidansa kuma tsohon shugaban APC ta kasa, Adams Oshimhole ne ya sa jam’iyyar ta ki ba shi damar sake takara a cikinta, matakin da ya sanya shi ya fice daga jam'iyyar.

Obaseki ya fafata da Osagie Ize-Iyamu na APC a zaben inda yayi nasarar lashe zaben a karo na biyu.

Mun dai ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta tabbatar da Mista Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Edo a karo na biyu bayan ya yi nasarar doke abokin karawarsa Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC.

Wannan shine karo na biyu da Obaseki ke yin nasara a kan Ize-Iyamu, inda a shekarar 2016 ma hakan ta kasance sai dai a lokacin Obaseki ya yi takara a karkashin APC yayin da Ize-Iyamu ke PDP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng