"Ba Za Ka Fadi Ba": Ganduje Ya Shiga Kano da Jiniya, Kanawa Sun Yi maraba da 'Uban Abba'

"Ba Za Ka Fadi Ba": Ganduje Ya Shiga Kano da Jiniya, Kanawa Sun Yi maraba da 'Uban Abba'

  • Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya koma mahaifarsa a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu
  • Ganduje, wanda shine shugaban APC na kasa ya kuma jagoranci taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a sakatariyar jam'iyyar da ke jihar
  • Kanawa sun yi masa kirari yayin da wasu manyan motoci da jiniya suka rufa masa baya zuwa sakatariyar jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A yammacin ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, ne tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya dira a garin Kano.

Wannan shine karo na farko Ganduje ke shiga mahaifar tasa tun bayan da ya sauka daga karagar mulki.

Ganduje ya sha kirari a wajen Kanawa
“Kurda ka shiga ko ina kaga dama”: Bidiyo sun bayyana yayin da Ganduje ya jagoranci taron APC a Kano Hoto: Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Shugaban na APC ya isa jihar ne domin halartan wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Babban labari: An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP na jiha 1, sahihan bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani bidiyo da ya yadu a dandalin soshiyal midiya, an gano jerin motoci da jiniya suna marawa babban jigon na APC baya a hanyarsu ta zuwa sakatariyar jam’iyyar da ke jihar, inda a nan ne za a gudanar da tyaton.

Ganduje ya sha kirari a wajen Kanawa

An kuma jiyo wata murya tana tashi daga bindiyon inda take ta kirari ga tsohon gwamnan. Abun da mutumin ke fadi kuwa shine:

“Mashaa Allahu uban Abba Ganduje, mashaa Allahu, shugaban jam’iyya Allah ya kara daraja.”

Tsohon dan takarar gwamnan Kano a zaben 2023, Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu shine ya wallafa bidiyon a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya.

Ya rubuta a shafin nasa:

“Kurda ka shiga ko ina kaga dama a garin ka Uban Jam'iya!”

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje ya nemi korar mutum 3 a APC, a dauko Kwankwaso daga NNPP

Haka kuma a wani bidiyon wanda @tudunwada__mi ya wallafa a shafinsa, an gano lokacin da Ganduje ya isa babban ofishin jam'iyyar da ke Kano. Ya rubuta a saman bidiyon:

"Ka bar Kano da jiniya sannan ka dawo da jiniya.
"Baba Ganduje Allah ba zai bar ka ba Insha'allahu."

Jama’a sun yi martani kan bidiyon Ganduje a garin Kano

@Abbadanejo ya ce:

"Haka Allah yaso ba yanda zasuyi da Kai.
"Hassadarda suke Maka tazaman Maka taki."

@AuwalAgenda ya yi martani:

"Sai yan kwankwassiyya sun fusata azo ana jaje ."

@sirsalim5"

"Mai daga hannu a titi shi ba a daga masa .
"Allah karaba mu da irin wannan siyasa nashigo garin amma jama a basu taroni ba."

@waziri79_:

"Ka ga Mota sai ka ce Tuwon Masara a ke bata ta ci shegiya. Kai gaskiya mulki na da daadi walla."

Legit Hausa ta ji ta bakin Kanawa kan dawowar Ganduje Kano da irin tarbar da ya samu.

Kara karanta wannan

Ganduje ya isa jihar Kano, zai gana da masu ruwa da tsaki kan batun sasantawa da Kwankwaso

Malama Zainab Ummi ta ce:

"Magana ta gaskiya Kanawa mun dawo daga rakiyar tsohon gwamnanmu, Abdullahi Ganduje, ko da ya dawo babu wani 'doki da kowa ya yi kan dawowarsa. Yawanci wadanda ka ga suna yi masa kirari ko wani duk yan kanzaginsa ne.
"Amma magana ta gaskiya talaka baya yin Ganduje a jihar Kano."

Muhammdu Sani kuwa cewa ya yi:

"Muna yi wa Ganduje fatan alkhairi, duk da rashin kyautawa ko wani abu da ake ganin ya yi a Kano, tsohon gwamnan namu ya bar abun da ba za a manta da shi ba.
"Kuma a ganina ya samu ci gaba tunda yanzu uban jam'iyya yake na kasa, ka ga kuwa bai tagayyara ba sai dai idan za a sako son zuciya."

Kwamishinan Ganduje ya nemi korar mutum 3 a APC

A wani labarin kuma, mun ji cewa Muazu Magaji Dansarauniya ya shaida cewa bai halarci taron manyan APC ba, wanda yace an yi a jihar Kano a yau Alhamis.

‘Dan siyasar ya tofa albarkacin bakinsa a Facebook, ya nuna bai goyon bayan shugabannin da ke rike da APC ta reshen Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng