Korarren kwamishinan Ganduje, Mu'az Magaji ya bayyana irin alakarsa ta yanzu da gwamnan
Tsohon kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa na jihar Kano, Injiniya Muazu Magaji Dansarauniya, ya ce har yanzu yana nan yana goyon bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano.
Ya ce a shirye yake wajen goyon bayan mulkinsa don samun cimma manufarsa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamna Ganduje ya sallami Dansarauniya a watan Afirilu bayan mummunan tsokacin da yayi a kafar sada zumuntar zamani, a kan marigayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Abba Kyari.
A yayin zantawa da manema labarai a gidansa da ke Kano a ranar Talata, Dansarauniya ya ce Ganduje babu shakka yana shugabancin da ya dace a jihar.
Ya ce, duk da hakan akwai bukatar samar da sabbin dabaru ta hanyar tsamo matasa tare da saka su a harkokin kimiyya, fasaha da sauran bangarorin siyasa, ma'aikatu da noma.
"Bai kamata a ce gwamnati ta rushe shagunan masu kananan kasuwanci ba, ba tare da basu wata mafita ba.
"Wannan barazana ce babba ga jam'iyyar mu saboda dole mu nemi goyon bayansu kamar yadda muka samu a baya," yace.
KU KARANTA: Bidiyo da hotuna: An yi jana'iza tare da birne Isma'ila Funtua a Abuja
A wani labari na daban, gwamnatin Jihar Kano ta soke bukukuwar babban sallah da aka saba yi duk shekara a jihar a bana kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakin ne domin cigaba da dakile yaduwar annobar COVID-19 duba da cewa an sassauta dokar zirga zirga a jihohi da dama har da Kano.
Kwamishinan labarai na jihar, Mallam Muhammad Garba yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Laraba ya ce an dauki matakin ne yayin taron Majalisar Zartarwa na Jihar da aka yi ranar Talata.
Ya ce duk da cewa an bayar da izinin yin sallar idi a jihar, za a gudanar da sallar ne bisa kaidojin da hukumomin lafiya suka bayar na tazara da saka takunkumin fuska da sauransu.
Garba ya kara da cewa dukkan sarakuna biyar na jihar za su tafi masalatan Idi a cikin motocinsu sannan babu ziyara zuwa gidan Shettima, Hawan Daushe, Hawan Nasarawa da sauran bukukuwa.
Hakazalika, gwamnati za ta taimaka wurin samar da kayayyakin tsare lafiya kamar takunkumin fuska, sinadarin wanke hannu, hand sanitizer, kuma za ta tabbatar mutane sun bayar da tazara a filayen sallar Idi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng