Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Karshe Kan Zaben Gwamnan APC, Komai Na Iya Faruwa
- Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Sokoto da ake takaddama a kai
- Kotun ta sanya yau Alhamis 25 ga watan Janairu don yanke hukuncin karshe kan shari'ar zaben gwamnan
- A baya, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmad Aliyu na APC a matsayin gwamnan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Jam'iyyun PDP da APC a jihar Sokoto na cikin zullumi yayin da suke dakon hukuncin Kotun Koli.
Kotun Koli ta shirya yanke hukuncin shari'ar zaben gwamnan jihar a yau Alhamis 25 ga watan Janairu, cewar Punch.
Wane hukunci aka yi a baya?
Idan ba manta ba, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmad Aliyu na APC a matsayin zababben gwamnan jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Sa'idu Umar saboda rashin gamsassun hujjoji, cewar Channels TV.
Daga bisani, Umar ya durfafi Kotun Koli don neman hakkinsa da aka kwace a Kotun Daukaka Kara.
Mambobin jam'iyyun APC da PDP a jihar sun nuna kwarin gwiwarsu ka wannan hukunci da za a yanke.
Martanin PDP da APC Kan shari'ar
Sakataren yada labaran PDP, Hassan Sentimental ya bayyana cewa su na da kwarin gwiwar samun nasara a kotun.
Ya ce:
"Muna da kwarin gwiwar samun nasara kotun a ranar Alhamis saboda hujjojin da muka gabatar.
"Sa yardar Allah madaukakin Sarki za mu samu adalci a kotun da za ta yanke hukunci."
Sai dai shugaban jam'iyyar APC a jihar, Isa Achida bai ce komai ba game da shari'ar da za a yanke a yau.
Ya ce bai kamata ya ce wani abu ba kan shari'ar da za a karkare ta ranar Alhamis, cewar Lagos Post Online.
Ya ce:
"Babu abin da zan iya cewa a kai a yanzu, shari'ar ta na gaban kotu kuma a gobe za a yanke ta, gaskiya ba zan iya cewa komai ba."
Kotu ta yi hukunci kan matsalar Majalisar Plateau
A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan shari'ar Majalisar jihar Plateau a Najeriya.
Kotun ta ce ba za ta tilasta kakakin Majalisar dakatar da sabbin 'yan Majalisun APC 16 ba.
Asali: Legit.ng