Atiku Abubakar Ya Koma Kotu da Tsohuwar Hadimar Buhari Kan Abin da Ya Faru Tun 2019

Atiku Abubakar Ya Koma Kotu da Tsohuwar Hadimar Buhari Kan Abin da Ya Faru Tun 2019

  • Atiku Abubakar yana neman Lauretta Onochie ta biya sa Naira biliyan 2 na cin zarafin sa da tayi
  • Kotun tarayya da ke Abuja ta zauna domin sauraron shari’ar amma lauyan wanda ake kara bai zo ba
  • Wadanda suka tayawa Alhaji Atiku sun bukaci alkali ya hukunta wanda yake kare Lauretta Onochie

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Wata babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta daga lokacin sauraron shari’ar Atiku Abubakar da Lauretta Onochie.

‘Dan takarar shugaban kasar na PDP a zabukan 2019 da 2023 yana shari’a da Lauretta Onochie, Daily Trust ce ta fitar da labarin dazu.

Atiku
Atiku Abubakar da Lauretta Onochie Hoto: @Atiku, @Laurestar
Asali: Twitter

A ranar Laraba, Alkali Chizoba Orji ya daga zaman shari’ar zuwa 25 ga watan Maris saboda rashin ganin lauya da yake bada kariya a kotu.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje ya nemi korar mutum 3 a APC, a dauko Kwankwaso daga NNPP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku: Lauyan Onochie bai je kotu ba

Madam Lauretta Onochie ta dauko hayar U.O. Sule (SAN) ne ya kare ta a karar da tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya shigar.

Lauyoyin Atiku, Dr Okey Ezugwu and S.E. Maliki sun bukaci a ci U.O. Sule (SAN) tarar N1m a matsayin hukuncin rashin mutunta zaman.

Wani abokin aikin babban lauyan mai bada kariya, C.O. Ogbodo Esq ya iso kotun a makare, ya nema masa uzuri a wajen Chizoba Orji.

Rahoton yace C.O. Ogbodo Esq ya fadawa kotu cewa U.C Sule SAN bai samu halartar zaman ba ne saboda ya tafi wani aiki a Sokoto.

Shari'ar Atiku v Lauretta Onochie a kotu

A Disamban 2019 ne Mike Ozekhome (SAN) ya kai kara a kotun tarayyan, yana tuhumar Onochie da yayi wa Alhaji Atiku sharri.

Kara karanta wannan

Dangote zuwa Otedola: Masu kudin Afrika 20 da adadin Dalolin da suka mallaka a 2024

Sa’ilin tana aiki a matsayin mai taimakawa Muhammadu Buhari, Onochie ta jefi Atiku da zargin ana nemansa saboda ta’addanci.

A cewar wannan mata, kasar UAE tana tuhumar Wazirin Adamawa da ta’addanci, jagoran adawan ya kai kara domin neman hakkinsa.

‘Dan takaran shugaban kasar yace abin da wannan mata ta fada ya jawo masa abin kunya, cin mutunci, wulakanci da tashin hankali.

Tinubu zai kori wasu Ministoci

Hadiza Bala Usman ta nanata cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gaske yake yi game da alkawuransa, ba zai bada kunya ba.

Saboda haka ne hadimar ta ce Tinubu zai auna ayyukan ministoci sannan za a sauke wasu ministocin tarayya idan ba suyi aiki da kyau ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng