An cigaba da yakin baka tsakanin Atiku Abubakar da yar gidan Buhari

An cigaba da yakin baka tsakanin Atiku Abubakar da yar gidan Buhari

Guda daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari akan sha’anin kafafen sadarwa na zamani, Lauretta Onochie ta mayar da kakkausar martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar game da barazanar da yayi na mata gaban kotu saboda zargin cin mutunci da bata mata suna da yace ta yi.

Atiku Abubakar ta hannun lauyansa, Mike Ozekhome ya nemi Lauretta ta janye zargin da tayi na cewa wai hadaddiyar daular larabawa na neman sa ruwa a jallo, inda yace ta nemi afuwansa, kuma ta buga neman afuwan a manyan jaridun Najeriya guda 6, ko kuma ta biyashi naira miliyan 500.

KU KARANTA: Wadanda suka yi garkuwa da surukar gwamnan jahar Katsina sun shiga hannu

An cigaba da yakin baka tsakanin Atiku Abubar da yar gidan Buhari

Atiku da Lauretta
Source: UGC

Sai dai Lauretta tayi fatali da wannan barazana na Atiku, inda ta bayyana hakan ga wani dabara da Atiku Abubakar da lauyoyinsa suke yi don ganin sun dauke mata hankali yayin da shari’ar zabe tsakanin Atiku da Buhari ya fara zafafa.

Yar gidan Buhari bata tsaya nan ba, inda ta cigaba da cewa a yanzu haka Atiku ya fada cikin matsanancin damuwa, don haka magani yake nema domin ya samu kansa ba shari’ar kwace mulki ba, amma hadimansa ba zasu taba fada masa saboda kare abincinsu.

“Miyagu ba zasu sake samun sararawa a Najeriya ba, ina kwananku yan uwa da abokan arziki, kada ku dauki wannan a matsayin raddi ga birkitaccen Atiku Abubakar wanda hadimansa suke masa ingiza mai kan turuwa a kullum domin samun damar cin abinci, a maimakon su bashi maganinsa.

“Ina sanar da masoyana da suka dinga kirana don bayyana damuwarsu ga barazanar da Atiku yayi min cewa ina nan kalau, kuma cikin koshin lafiya, sai dai ma dariya nake yi ma wawayen da suke kokarin taboni, yaro bai san wuta ba sai ya taka.

“Manufarsu itace su kawar da hankalina daga shari’ar da Atiku ya shigar da Buhari a kotun sauraron korafe korafen zabe, toh su sani basu isa ba, magoya bayan Buhari miliyan 34 na nan daram dam dam.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel