An Samu Damuwa Yayin da INEC Ta Hango Babbar Matsala Ana Daf da Gudanar da Zabe a Watan Gobe
- Hukumar zabe ta INEC ta sanar da cewa akai rahotanni da suke nuna samun tashe-tashen hankula a zaben da za a gudanar
- Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu shi ya bayyana haka a yau Talata 23 ga watan Janairu a Abuja
- Yakubu ya ce mafi yawan irin wannan zaben cike gurbi na zuwa da kalubale don haka dole za a kula sosai kan zaben
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce akwai alamun tada kayar baya a zaben da za a gudanar.
Yakubu ya ce sun samu rahoton kawo tsaiko a zaben cike gurbi da za a gudanar a ranar 3 ga watan Faburairu.
Wane matsala INEC ta hango?
Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a yau Talata 23 ga watan Janairu a Abuja yayin wata ganawa da kwamitin tsaro na zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesan ya ce mafi yawan irin wannan zaben cike gurbi na zuwa da kalubale don haka dole za a kula sosai kan zaben, cewar Daily Trust.
Ya ce:
“Daga darasin da muka samu a baya, gudanar da zabe irin wannan ya na cike da kalubale da kuma matsaloli.
“Dole za mu kula sosai musamman ganin yadda ake yawan samun matsaloli kan irin zabukan daga ‘yan takara da magoya baya.
“Daga rahotanni da muke samu, akwai damuwa kan yanayin tsaro da ke kara kamari a wasu jihohi a yayin gudanar da zaben.”
Wane gargadi INEC ta yi?
Yakubu ya kalualanci jami’an tsaro da su samar da yanayi mai kyau don samun gudanar da zaben cikin lafiya.
Ya ce za a gudanar da zaben kashi biyu, na farko zaben cike gurbi wanda masu kujerun suka mutu ko kuma suka yi murabus a Majalisun jihohi da Tarayya.
Sannan na biyu shi ne wanda za a sake zaben saboda hukuncin kotunan kararrakin zabuka yayin shari’o’i, cewar Vanguard.
Ya kara da cewa zabukan sun shafi mazabun Majalisar Dattawa guda biyu da Majalisar Wakilai guda hudu sai Majalisar jihohi guda uku.
INEC ta sanar da ranar zabe
A wani labarin, Hukumar zabe ta fitar da ranar gudanar da zabukan cike gurbi a Najeriya baki daya.
Hukumar ta ce ta sanya 3 ga watan Faburairu a matsayin ranar gudanar da zaben cike gurbi.
Asali: Legit.ng