INEC Ta Saka Ranar Sake Zabe Don Cike Gurbin Kujerun da Kotu Ta Rushe da Sauransu, Ta Tura Gargadi

INEC Ta Saka Ranar Sake Zabe Don Cike Gurbin Kujerun da Kotu Ta Rushe da Sauransu, Ta Tura Gargadi

  • Hukumar INEC ta fitar da ranar sake zabe don maye gurbin kujerun ‘yan siyasa da dama a kasar saboda wasu dalilai
  • Hukumar ta sanar da ranar 3 ga watan Faburairu don gudanar da zabukan da suke babu kowa ko wadanda kotu ta yi umarni a kansu
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan wayar da kan jama’a, Sam Olumekun ya fitar a yau Juma’a 22 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, AbujaHukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta fitar da sabuwar sanarwa kan sake zabubbuka a wasu mazabu a fadin kasar.

INEC ta sanar da ranar 3 ga watan Faburairu don gudanar da zabukan da suke babu kowa ko wadanda kotu ta yi hukunci a kansu.

Kara karanta wannan

Rusa zaben Abba Kabir: Jerin hukunce-hukuncen kotu 4 da suka bai wa kowa mutane a 2023

INEC ta saka ranar sake zaben cike gurbin kujerun da aka rushe
INEC ta tabbatar da ranar 3 ga watan Faburairu don gudanar da zaben cike gurbi. Hoto: INEC Nigeria.
Asali: Getty Images

Yaushe za a gudanar da zaben?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan wayar da kan jama’a, Sam Olumekun ya fitar a yau Juma’a 22 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sam ya ce sake zaben ya kunshi kujerun sanatoci biyu da Majalisar Wakilai hudu da kuma Majalisun jihohi guda uku.

Har ila yau, Sam ya ce wandannan zabukan da za a sake sun shafi jihohi tara da ke fadin kasar baki daya.

Sake zaben zai gudana ne a mazabu 35 da ke fadin kasar wadanda suka hada da zabukan da suka shafi hukuncin kotunan zabe.

Wane gargadi INEC ta yi?

Hukumar ta kirayi dukkan jam’iyyun kasar da su bi dokokin jadawalin zabukan da ta fitar don samun abin da ake nema.

Wannan na zuwa ne bayan wasu kotunan zabe sun ba da umarnin sake zabuka a wasu mazabu da suka ayyana wanda bai kamala ba.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun ta tsare matashi kan zargin caka wa abokinsa wuka a ciki, wanda ake zargi ya magantu

Har ila yau, akwai kujerun da shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai suka ayyana su babu kowa, cewar Tribune.

Dukkan zabukan kuma da aka lissafo za a gudanar da su ne a ranar 3 ga watan Faburairun sabuwar shekara.

INEC ta sanar da shirin gudanar da zabe

A wani labarin, Hukumar INEC ta sanar da sake zabuka don cike gurbin wasu kujeru a fadin kasar.

INEC ta sanar da hakan ne don cike gurbin kujerun da babu kowa a kansu a Majalisun Tarayya da na jihohi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel