Tinubu Ya Bayyana Babban Dalilinsa Na Kin Rage Yawan Ministoci Daga 47, Ya Shawarci Malaman Addini

Tinubu Ya Bayyana Babban Dalilinsa Na Kin Rage Yawan Ministoci Daga 47, Ya Shawarci Malaman Addini

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilin kin rage yawan Minstoci a Najeriya inda ya ce hakan ba zai haifar da abin da ake so ba
  • Tinubu ya ce ya ki rage ma'aikatun ne saboda babu abin da haka zai haifar sai rashin kawo ci gaban kasa
  • Shugaban ya bayyana haka a yau Litinin 22 ga watan Janairu yayin ganawa da Kungiyar Kiristoci ta CAN

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya saka bai rage yawan ma'aikatu ba.

Tinubu ya ce ya ki rage ma'aikatun ne saboda babu abin da haka zai haifar sai rashin kawo ci gaban kasa, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Bam ya raunata yara 10 a Kaduna, bayanai sun fito

Tinubu ya fadi dalilin kin rage yawan ma'aikatu a Najeriya
Tinubu shawarci malaman addini kan koyarwa ta gaskiya. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Mene dalilin Tinubu kan ma'aikatu?

Ya ce dalilin shi ne duk lokacin da aka daura wa mutum daya nauyin ma'aikatu biyu ko uku ba zai ba da sakamakon da ake bukata ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya bayyana haka a yau Litinin 22 ga watan Janairu yayin ganawa da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), cewar Leadership.

Har ila yau, Tinubu ya shawarci malaman addinin da su rinka koyar da mutane abin da ya dace inda ya ce hakan shi ne taimakon kasar.

Hadimin shugaban a bangare yada labarai, Ajuri Ngelale ya ce Tinubu ya kuma bayyana himmatuwarsa wurin yaki da cin hanci a kasar.

Wace shawara Tinubu ya bayar?

Yayin da ya ke bayyana amfanin malaman addini a kasar, ya bukaci shugabannin addinin Kirista da su ba shi goyon baya a yaki da cin hanci.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ganawa kan matsalar tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu ya nada dan Arewa babban mukami

Sanarwar ta ce:

"Ba mu da wata kasa kamar Najeriya, idan har ba ku koyar da fahimtar da juna da zaman lafiya ba, kuna bata kasar ce kuma babu mai gyara ta.
"Dole mu yi zama saboda yawan kushe kasar ba shi ne zai gyara 'yan kasar ba, dole mu rinka shawartar 'yan Najeriya su sauya tunaninsu.
"Dole ku nuna wa 'yan Najeriya kada su mayar da son kudi kamar abin bauta, hakan shi zai kai mu ga tudun mun tsira."

Dattawan APC a Kano sun shawarci Tinubu

Kun ji cewa dattawan jam'iyyar APC a jihar Kano sun bai wa Shugaba Tinubu shawara kan kirar korar shugaban jam'iyyar, Umar Ganduje.

Dattawan sun yi wannan kiran ne yayin da wasu matasa suka bukaci shugaban ya kori Ganduje daga mukaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.