Tinubu: Sanatocin Jihohin Arewa Za Su Yaki ‘Rashin Adalcin’ Da Ake Yi Mana, Kawu Sumaila
- Sanatocin da suka fito daga Arewa sun nuna rashin goyon baya kan dauke hedikwatoci daga birnin tarayya
- Sanata Suleiman Kawu Sumaila ya fitar da jawabi cewa za su karbawa al’ummarsu hakki a gwamnatin sama
- Ana zargin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kawo tsare-tsaren da ba su fifita mutanen Arewacin kasar nan
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Sanatocin Arewa sun nuna rashin amanna da dauke wasu ofisoshi da za ayi daga birnin tarayya na Abuja zuwa garin Legas.
Sanatocin da ke wakiltar jihohin Arewacin kasar a majalisar dattawa sun fitar da matsaya a ranar Litinin, Daily Trust ta kawo rahoton.
Kungiyar sanatocin yankin na Arewa sun soki gwamnati, suka yi kira ga al’ummar da suke wakilta suyi hakuri a cin ma matsaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatoci za su zauna da Tinubu?
‘Yan majalisar sun nuna za su zauna da gwamnatin tarayya domin a tattauna da nufin a bar ofisoshin a Abuja da ta ke birnin tarayya.
Idan abin ya gagara, The Guardian ta ce ‘yan majalisar dattawan sun shirya kai karar gwamnatin Bola Tinubu a kotu a raba masu gardama.
Jawabin Sanatocin ya fito ne ta bakin kakakinsu watau Sanata Suleiman Kawu Sumaila.
Bangaren jawabin Sanatocin Arewa
"A matsayin wakilan al’umma a matakin kasa (majalisar dattawa), a shirye muke wajen shawo kan abin da ya damu mutanen mazabunmu game da wasu matakai da tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta kawo – daga son kai wajen rabon albarkatu zuwa dauke wasu ma’aikatu daga Abuja zuwa Legas."
- Suleiman Kawu Sumaila
Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila yace za a bi hanyar lalama ko ta shari’a idan ta kama.
Buba Galadima ya hangowa Arewa
Da Legit Hausa ta tuntubi Buba Galadima wanda jagora ne a NNPP, yace sai da suka ankarar da talaka a kan halin da za a burma ciki.
Injiniya Galadima yake cewa sun ja-kunnen al’umma lokacin zaben 2023 cewa idan APC ta ci zabe za a karya Abuja domin karfafa Legas.
Dattawan Arewa sun soki dauke CBN, FAAN
An ji babban bankin kasa watau CBN zai maida wasu manyan ofisoshinsa zuwa Legas, dattawan Arewa sun soki wannan yunkuri.
Bayan haka sai aka ji Festus Keyamo ya bada umarnin dauke hedikwatar FAAN daga birnin Abuja, za ta koma Legas da aka sani a baya..
Asali: Legit.ng