Korarrun 'Yan Majalisu 16 Sun Sha Alwashin Komawa Kujerunsu Karfi da Yaji, Sun Fadi Dalilansu

Korarrun 'Yan Majalisu 16 Sun Sha Alwashin Komawa Kujerunsu Karfi da Yaji, Sun Fadi Dalilansu

  • Sabon rikici ya tashi yayin da korarrun 'yan Majalisu suka sha alwashin komawa kujerunsu karfi da yaji
  • Kotun Daukaka Karar ta rusa zaben 'yan Majalisun 16 da hujjar jami'yyarsu ta PDP ba ta da tsarin daukar nauyinsu a zabe
  • Legit ta ji bakin wani dan jam'iyyar PDP da ke Jos kan wannan rikicin da hukuncin kotun ya jawo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Rikicin siyasa na kara tsami a jihar Plateau tun bayan rusa 'yan Majalisu 16 da Kotun Daukaka Kara ta yi.

Korarrun 'yan Majalisun sun sha alwashin komawa kan kujerunsu duk da hukuncin Kotun Daukaka Kara.

'Yan Majalisu 16 da aka kora a Plateau sun sha alwashin komawa kujerunsu
Korarrun 'yan Majalisu 16 sun sha alwashin komawa kujerunsu. Hoto: Plateau House of Assembly.
Asali: UGC

Wane hukunci kotun ta yanke a baya?

Kara karanta wannan

Kano: Bayan DSS ta cafke Dan Bilki, kotu ta dauki mataki kan zargin cin zarafin Kwankwaso

Kotun Daukaka Karar ta rusa zaben 'yan Majalisun ne guda 16 da hujjar jami'yyarsu ta PDP ba ta da tsarin daukar nauyinsu a zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Kotun Koli kuma ta tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Mutfwang wanda ya fito jami'yya daya da 'yan Majalisun, cewar Daily Trust.

'Yan Majalisu sun bayyana haka ne a yau Litinin 22 ga watan Janairu yayin hira da 'yan jaridu a Jos babban birnin jihar Plateau.

Jaboran 'yan Majalisun, Ishaku Maren ya ce tun da Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Caleb su ma su na da damar komawa kujerunsu.

Martanin Gwamna Caleb kan lamarin

Sun tabbatar da cewa za su koma Majalisar a ranar Talata 23 ga watan Janairu lokacin da Majalisar za ta koma bayan hutun watanni biyu.

A ranar Juma'a ce 19 ga watan Janairu Gwamna Caleb na jihar ya kai ziyara ga Shugaba Tinubu kan lamarin, cewar Platinum Post.

Kara karanta wannan

Abin takaici ne, Babban lauya ya soki Abba Kabir da gwamnoni bayan nasara a Kotun Koli, akwai dalili

Caleb bayan ziyarar ya bayyana cewa duk wani mataki na siyasa da shari'a an dauka don kwato musu hakkinsu.

Idan ba a mantaba, a ranar 12 ga watan Janairu ce Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Mutfwang a matsayin zababben gwamnan jihar.

Muhammad Sani Ahmed ya shaidawa Legit Hausa cewa akwai rantsar rashin adalci a hukuncin kotun.

Sani ya ce:

"Babban abin dubawa shi ne yadda Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar Gwamna Caleb.
"Shin shi ba daga jam'iyyar PDP ya ke ba? Kamar yadda ya fada dole a sake zama."

Sai dai ya shawarci 'yan Majalisar da su bi hanyar da ta dace don neman hakkinsu.

Gwamna Caleb ya tura sako ga alkalai

Kun ji cewa, Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya bukaci a sake zama kan hukuncin da ya rusa zaben 'yan Majalisun jihar da na Tarayya.

Caleb ya yi wannan kira ne bayan Kotun Koli ta tabbatar da shi a matsayin zababben gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.