Kamar Tinubu, Gwamnan Arewa Ya Amince da Biyan Ma’aikata N35,000 Don Rage Radadin Cire Tallafi

Kamar Tinubu, Gwamnan Arewa Ya Amince da Biyan Ma’aikata N35,000 Don Rage Radadin Cire Tallafi

  • Yayin da ake ci gaba da karbar kaya bayan cire tallafin mai a Najeriya, Gwamna Buni na jihar Yobe ya dauki mataki
  • Gwamnan ya amince da biyan naira dubu 35 ga ma'aikatan gwamnatin jihar don rage musu radadin cire tallafi
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban ma'aikatan jihar, Hamidu M. Alhaji ya sanya wa hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da biyan ma'aikata naira dubu 35 don rage musu radadin cire tallafi.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban ma'aikatan jihar, Hamidu M. Alhaji ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Kano: Tashin hankali yayin da matashi ya sheke abokin aikinsa a Kamfani, matasa sun tafka barna

Gwamnan Arewa ya amince da biyan naira dubu 35 ga ma'aikata
Gwamnan Buni Ya Amince da Biyan Ma’aikata N35,000 Don Rage Radadi. Hoto: Mai Mala Buni.
Asali: Twitter

Mene Buni ya amince da shi?

A cikin sanarwar, gwamnan ya amince da nadin Sakataren Gwamnatin jihar, Baba Malam Wali a matsayin shugaban kwamitin kula da biyan kudaden.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, gwamnan ya ce kwamitin na dauke da mambobi shida don tabbatar da ba da kudaden ba tare da matsala ba.

Kwamitin sun hada da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar da kwamishinan ma'aikatar kudade a jihar, cewar Daily Trust.

Sauran sun hada da shugaban kungiyar kwadago ta NLC a matsayin mamba da kuma shugaban kungiyar TUC.

Aikin da kwamitin zai yi

Kwamitin zai kula da lamarin yawan kudaden da za a kashe a kokarin biyan kudin tare da zama da kungiyar Kwadago kan lamarin.

Wannan na zuwa ne bayan cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayun shekarar 2023, cewar National Insight News.

Kara karanta wannan

Tallafin COVID-19: Gwamnatin Jigawa ta dakatar da jami’an da aka kama da laifin karkatar da N1.7bn

Cire tallafin mai din ya jefa mutanen kasar cikin mummunan mawuyacin hali da tsadar kayayyakin masarufi.

Buni ya gana da Tinubu a fadarsa a Abuja

A wani labarin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya gana da Shugaba Bola Tinubu a fadarsa da ke birnin Tarayyar Nigeria, Abuja.

Alhaji Mahmud Muhammad, daraktan yada labaran gwamnan shi ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.

Wannan ziyarar da Gwamna Buni ya kai bai rasa nasaba da yawan hare-haren 'yan ta'adda a jihar baki daya dama Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.