Abdullahi Ganduje Ya Rufe Ido, Ya Fallasa Masu Kawo Matsala a Lokacin Zabe

Abdullahi Ganduje Ya Rufe Ido, Ya Fallasa Masu Kawo Matsala a Lokacin Zabe

  • Ana samun kalubale wajen shirya nagartaccen zabe, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ba laifin INEC ba ne
  • Shugaban APC na kasa ya jefi abokan aikinsa watau ‘yan siyasa da kawo matsala wajen harkar zabe
  • Dr. Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne lokacin da wasu jami’an INEC suka ziyarci hedikwatar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya zargi abokansa ‘yan siyasa da hannu wajen tada zaune tsaye a siyasa.

Duk rigingimun da ake samu wajen zabe, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana ganin laifin ‘yan siyasa ne, Vanguard ta kawo rahoton.

Abdullahi Umar Ganduje
Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: @Dawisu
Asali: Twitter

INEC ta ziyarci Abdullahi Ganduje a APC

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana matsayarsa a lokacin da jami’an hukumar zabe na INEC suka ziyarce shi a sakatariyar APC.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana jiha 1 tal da jam'iyyar APC za ta kwato daga hannun PDP a 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da yake magana a ranar Laraba, shugaban na APC ya wanke INEC daga zargi, ya ce ‘yan siyasa suke jawo hayaniya a zabe.

"Na san cewa babbar matsalar hukumar INEC wajen gudanar da zabe shi ne rashin tsaro. Kowa zai ce INEC, amma ‘yan siyasa ne."
"Saboda haka domin fahimtar dokoki da ka’idojin zabe, a fahimci abin da ake bukata, cibiyarmu za ta rika wayar da kan mutane."
"Idan ba da hadin-kan ‘yan siyasarmu ba, za a lallata lamarin."

-Abdullahi Umar Ganduje

Punch ta ce Dr. Abdullahi Ganduje ya jinjinawa ma’aikatan INEC da suka kawo masu ziyara, ya kuma bayyana masu irin shirin APC.

APC a karkashin Abdullahi Ganduje

Baya ga lashe zabe, shugaban na APC yana kokarin ganin jam’iyyarsa ta taka rawar gani wajen inganta siyasa da tsarin damukaradiyya.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10, APC ta fadi wanda ya taimakawa Buhari ya samu takarar cin zabe

Ganduje ya ce sun umarci shugabannin jam’iyya a matakan mazabu, kananan hukumomi, jihohi da kuma shiyyoyi su dage a aikinsu.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce APC ta kawo fasahar zamani wajen yi wa daukacin ‘ya ‘yanta rajista tare da hada-kai da INEC.

Soyinka da zargin zaben 2023

An rahoto Wole Soyinka yana ikirarin saura kiris tarihi ya maimaita kan shi, wasu mutane sun dage sai sun kawo tasgaro a zaben 2023.

Farfesa Soyinka yana zargin an shirya makarkashiya tun farko kafin zaben domin a tabbatar da ba ayi zaben shugaban kasa a bara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel