Ganduje Ya Bayyana Jiha 1 Tal Da Jam'iyyar APC Za Ta Kwato Daga Hannun PDP a 2024

Ganduje Ya Bayyana Jiha 1 Tal Da Jam'iyyar APC Za Ta Kwato Daga Hannun PDP a 2024

  • Dakta Abdullahi Ganduje ya ce APC ta kudiri aniyar kara yawan jihohin da take mulki a Kudu maso Kudu ta hanyar kwace jihar Edo
  • Shugaban APC na ƙasa ya ayyana cewa dama tun asali Edo ta jam'iyyar APC ce don haka zasu kwato ta a zaben gwamna a 2024
  • Ranar 21 ga watan Satumba, 2024 INEC ta tsara yin zaben gwamna a Edo yayin da APC zata tsaida ɗan takara a watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban All Progressives Congress (APC), Dakta Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa jam'iyya mai mulki ta fara shirye-shiryen kwato mulkin jihar Edo a 2024.

Ganduje ya yi wannan furucin ne a wurin taron masu ruwa da tsakin APC na jihar Edo da mambobin kwamitin gudanarwa na kasa da ya gudana a Abuja ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Bayan rasa kujerar Kano, Ganduje ya tafka asara bayan shugaban APC ya yi murabus, an fadi dalili

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
Ganduje Ya Bayyana Jiha Ɗaya Tal ɗa Jam'iyyar APC Zata Kwace Daga Hannun PDP a 2024 Hoto: OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Shugaban jam'iyya mai mulkin ya jaddada cewa dama tun asali jihar Edo ta APC ce, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) sanya ranar 21 ga Satumba, 2024, domin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo.

Jam’iyyar APC za ta zabi dan takararta na gwamna a zaben fidda gwani da ta tsara yi ranar 17 ga watan Fabrairu, 2024, jaridar PM News ta rahoto.

Abin da ya sa zamu karɓe jihar Edo - Ganduje

Da yake tsokaci kan shirin kwato jihar daga hannun PDP, Ganduje ya ce:

"Edo jiha ce ta APC, a yanzu ya zama dole mu dawo da Edo hannun mu. Jam'iyya mafi girma a faɗin Afirka na da jiha guda ɗaya kacal ne daga Kudu maso Kudu, ba zamu yarda da haka ba.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC na ƙasa ya bayyana jiha 1 da zasu ƙwace daga hannun PDP a 2024

"Jihar Kuros Riba ne kawai ke hannun mu bayan mun tsallaka koguna da dama, mun samu nasarar karɓe jihar Kuros Riba. Amma jihar Edo dole ne mu kwato ta.”

Dangane da adadin ‘yan takarar da suka nuna sha'awar tikitin takarar gwamnan APC a Edo, tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana cewa:

"Abin da nake hange shi ne da zamu hakura mu cimma matsaya ta hanyar yarjejeniya, ina ganin zai fi mana alheri."

Wani masoyin Ganduje kuma mamban APC a Kano, Shehu Wada, ya shaida wa Legit Hausa cewa yana da kwarin guiwa a kan shugabancin Ganduje.

A cewarsa, duk da wasu na ganin alamar mutuwar APC ne miƙa ragama hannun tsohon gwamnan Kano, amma a hasashensa ba su san asalin abin da Ganduje zai iya bane.

Ya ce:

"Wannan abu ne mai sauki a wurin Ganduje, ina da yaƙinin zai jagoranci APC ta lashe zaben Edo. Mutane na ganin ba zai iya ba saboda abinda ya faru a 2019, ba su san shi bane."

Kara karanta wannan

Ganduje ya gamu da rudanin takarar farko a APC tun bayan zama shugaban jam’iyya

Kotun koli zata yi hukunci a shari'ar zaben Sakkwato

A wani rahoton kuma Kotun koli ta tanadi hukunci kan ƙarar da jam'iyyar PDP ta nemi a tsige Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato daga kan mulki.

Kwamitin alkalai 5 karƙashin mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ne ya ɗauki matakin a zaman ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel