Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Neman Kifar da Gwamnan Arewa, Ta Fadi Dalilai
- Kotun Koli a Abuja ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa a yau Talata
- Kotun ta kammala sauraran dukkan korafe-korafen bangarorin guda biyu inda ta ce za a tuntube su kan hukuncin karshe
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan jam'iyyar APC a Lafia kan hukuncin kotun da aka yanke a yau
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa a yau Talata 16 ga watan Janairu.
Yayin zamanta a yau a birnin Tarayya, kotun ta tanadi hukunci kan shari'ar da ake yi don neman tsige Gwamna Sule Abdullahi.
Wane hukunci kotun ta yanke a baya?
Dan takarar jam'iyyar PDP, David Ombugadu shi ke kalubalantar zaben gwamnan jihar da cewa an tafka magudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ombugadu ya yi nasara a kotun sauraran kararrakin zabe kafin ya sha kaye a Kotun Daukaka Kara, cewar The Nation.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Sule Abdullahi na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Har ila yau, ta yi fatali da hukuncin karamar kotun inda ta ce ta yi hukunci ne bisa kuskure kan takaddamar zaben, cewar Channels TV.
Wane mataki kotun ta dauka?
Mai Shari'a, Kudirat Kekere-Ekun wacce ke jagorantar alkalan ta tabbatar da haka bayan sauraran korafe-korafen daga dukkan bangarorin.
Kudirat ta tanadi hukunci kan shari'ar inda ta ce za su sanar da dukkan bangarorin biyu da zarar an kammala duba shari'ar.
Har Ila yau, Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Ta kuma yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar APC, Nentawe Goshwe bayan samun nasara a kotun baya.
Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan APC a Lafia, Aminu Abdullahi:
Aminu ya ce su na da kwarin gwiwar samun nasara a zaben ganin yadda hukuncin baya ya nuna.
Ya ce:
"Kamar yadda muka yi nasara a Kotun Daukaka Kara haka zamu sake karbar kujerar a Kotun Koli."
Ya kara da cewa Gwamna Sule ya cancanci kujerar don karisa ayyukan alkairi da ya fara a jihar.
Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci a zaben Nasarawa
A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Sule Abdullahi na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen zababben gwamna.
Har ila yau, ta yi watsi da hukuncin karamar kotun da ta ayyana dan takarar jam'iyyar PDP, David Ombugadu a matsayin gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng