Mutane 6 da Suka Taimakawa Abba Kabir Yusuf Wajen Samun Nasarar Kotun Koli

Mutane 6 da Suka Taimakawa Abba Kabir Yusuf Wajen Samun Nasarar Kotun Koli

  • Abba Kabir Yusuf ya ware wasu mutane, ya gode masu da aka ayyana shi a matsayin halataccen gwamna
  • John Inyang Okoro da wasu abokan aikinsa ne na farko wajen tabbatar da mulkin NNPP da hukuncinsu
  • Gwamnan jihar Kano ya yabi shugaba Bola Tinubu ganin irin yadda gwamnatinsa ta saki marar kotun koli

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Abba Kabir Yusuf ya tsira da kujerarsa a matsayin gwamnan jihar Kano bayan hukuncin kotun kolin Najeriya.

Rahoton nan ya kawo sunayen wadanda suka taimakawa Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kano.
Gwaraza a shari'ar gwamnan Kano Hoto: @Dolusegun16, tekedia.com
Asali: UGC

Su wanene su ka ceci Abba Kabir Yusuf a Kano?

1. John Inyang Okoro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Hadimin Abba Ya Ware Mutum 6 a APC, Ya Jinjina Masu Kan Nasarar NNPP

Alkalan Kotun koli biyar a karkashin jagorancin John Inyang Okoro sun rusa hukuncin baya, suka maida Abba Kabir Yusuf a mulki.

Alkalan sun halattawa NNPP cin kuri’u 165, 600 da aka soke mata kuma tayi watsi da batun halaccin shiga takarar Abba Kabir Yusuf a 2023.

2. Bola Ahmed Tinubu

An jinjinawa shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna dattaku, ya kyale alkalan Kotun Koli su zartar da hukuncin da ba zai yi wa jam’iyyarsa dadi ba.

3. Kashim Shettima

Abba Kabir Yusuf ya yabi Kashim Shettima da kan shi a wani jawabi da ya fitar, ana tunani mataimakin shugaban kasar ya bi layin mai gidan na sa.

4. Wole Olanipekun

Oluwole Olanipekun, SAN ya canza lamarin shari’ar gwamnan Kano da ya karbi karar daga hannun lauyoyin NNPP a kotun sauraron korafin zabe.

Babban lauyan wanda yana cikin wadanda ake ji da su a Afrika ya wargaza soke takarar Abba a NNPP da hujjojin APC a kan kuri’un nan 165, 616.

Kara karanta wannan

Bayan ya koma Kano, Gwamna Abba ya faɗi mutum 1 da ya cancanci yabo kan hukuncin kotun ƙoli

5. AB Mahmud

A.B. Mahmoud ne lauyan da ya kare hukumar INEC a shari’ar zaben gwamnan Kano, ya bada gudumuwa sosai a rusa hukuncin da aka yi a baya.

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin na Najeriya ya tsaya tsayin-daka, ya gamsar da kotu kuri’un da aka sokewa NNPP daga hannun INEC suka fito.

6. Rabiu Musa Kwankwaso

Dole a jinjinawa Rabiu Musa Kwankwaso da wasu jagororin NNPP na kasa da suka dage tun farko wajen ganin Abba Kabir Yusuf ya yi nasara a 2023.

Kwankwaso ya bada gudumuwa sosai domin a hana APC karbe mulkin jihar Kano a kotu.

Kotun Koli: Maganar Muhammadu Sanusi II

Khalifan Tijjaniya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II ya zargi APC da rungumar kaddarar karya bayan neman karbe mulki da karfin tsiya.

Sanusi ya ce tun da a mulkin farar hula ake yi ba na mallaka ba, al’umma suke da hakkin zaben shugabanninsu ba tare da an zalunce su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng