Bayan Sha da Kyar a Kotun Koli, Gwamnan Arewa Ya Yi Alfaharin Shi Jarumi Ne Ba Ya Tsoron Artabu

Bayan Sha da Kyar a Kotun Koli, Gwamnan Arewa Ya Yi Alfaharin Shi Jarumi Ne Ba Ya Tsoron Artabu

  • Gwamna Bala Mohammed ya yi godiya ga magoya bayan jam'iyyar PDP da 'yan jihar Bauchi
  • Gwamna ya bayyana haka ne inda ya ke cewa shi jarumi ne wanda bai taba tsoron artabu ba a rayuwarsa
  • Ya bayyana haka yayin da ya ke jawabi ga dandazon 'yan jihar da suka tarbe shi bayan dawo wa daga Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Bayan ya yi nasara a Kotun Koli, Gwamna Bala Mohammed ya yi alfahari kan gwagwarmayar da ya yi.

Gwamna Bala ya bayyana cewa shi jarumi ne wanda bai taba tsoron artabu ba a rayuwarsa, cewar Tribune.

Gwamnan Arewa ya yi alfahari bayan nasara a Kotun Koli
Kauran Bauchi ya yi godiya ga 'yan jihar bayan nasara a Kotun Koli. Hoto: Bala Mohammed.
Asali: Facebook

Mene Kaura ke cewa a Bauchi?

Kaura ya bayyana haka a jiya Asabar 13 ga watan Janairu a Bauchi yayin da magoya bayansa su ka tarbe shi bayan dawo wa daga Abuja.

Kara karanta wannan

Kano: Mota ta murkushe mai kwacen waya jim kadan bayan fauce wayar wata, ya shiga kakani-kayi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Wasu manyan jihar Bauchi sun yi kutun-kutun don Gwamnatin Tarayya ta dauke ni a matsayin matsala.
"Sun manta cewa ni jarumi ne, Kauran Daular Usmaniyya."

Idan ba a mantaba Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya karrama gwamnan da sarautar Kauran Daular Usmaniyya.

Gwamnan ya ce tun da aka rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a ranar 29 ga watan Mayu bai taba barin jihar na tsawon kwanaki takwas ba.

Wane alkawari Kaura ya yi?

Ya ce ya kwashe kwanaki takwas a Abuja ne saboda kokarin ganin ba a zalunci mutanen jihar Bauchi ba, Newstral ta tattaro.

Ya kara da cewa:

"Ni jarumi ne tun daga haihuwa, na fito daga kauye, daga gidan sarauta amma kuma gidan malamai masu ilimi.
"Ina daya daga cikinku, ni ba dan ci rani ba ne ko dan kasuwa, amma ni bawanku ne."

Kara karanta wannan

Ba kamar Ganduje ba, Ministan Tinubu ya amince ya yi aiki tare da gwamnan jiharsa, ya fadi dalili

Kaura ya ce babban nauyin da ya ke kansa shi ne bautawa 'yan jihar saboda sun nuna masa kauna da soyayya.

Kaura ya yabawa Tinubu bayan hukuncin Kotun Koli

A wani labarin, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bayan yanke hukuncin Kotun Koli.

Kaura ya ce Tinubu ya na da girma a zuciyarsa ganin yadda bai tsoma baki a hukuncin kotun ba.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya samu nasara a Kotun Koli kan shari'ar zaben jihar da ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.