APC Ta Sadaukar da Kujerar Gwamnan Kano Ga Abba Kabir Ne Don Gudun Fitina? Gaskiya Ta Fito

APC Ta Sadaukar da Kujerar Gwamnan Kano Ga Abba Kabir Ne Don Gudun Fitina? Gaskiya Ta Fito

  • Jam’iyyar APC a kasa ta yi magana kan zargin ta bar wa Abba Kabir kujerar gwamna don gudun fitina
  • Jam’iyyar ta ce maganar da ake yadawa wai ta sadaukar da Kano don gudun tashin hankali babu kamshin gaskiya a ciki
  • Hakan ya biyo bayan jita-jitar cewa wani shiri ne aka yi don bar wa Gwamna Abba Kabir kujerarshi a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Jam’iyyar APC ta yi martani kan jita-jitar ta siyar da Kano bayan yanke hukuncn Kotun Koli kan zaben jihar.

Jam’iyyar ta ce maganar da ake yadawa wai ta sadaukar da Kano don gudun tashin hankali babu kamshin gaskiya a ciki.

Kara karanta wannan

Cikakkun sunaye: Abba Yusuf, Caleb Mutfwang da gwamnoni 8 da Kotun Koli ta tabbatyar da nasarorinsu

APC ta yi martani kan zargin sadaukar da hukuncin zaben Kano
APC ta musanta sadaukar da shari'ar Kano don gudun fitina. Hoto: Abdullahi Ganduje, Bola Tinubu, Rabiu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Mene APC ke cewa kan shari'ar Kano?

Nze Chidi Duru, mataimakin sakataren jam’iyyar ta kasa shi ya bayyana haka a yau Lahadi 14 ga watan Janairu, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tabbas jam’iyyar za ta so yin nasara a Kano amma kuma dole ta yi biyayya ga hukuncin kotun da ta yi.

Duru ya ce wannan hukunci na kotu ne kuma babu tantama za su bi shiyasa ake da kotuna idan bai gamshe ka ba ka daukaka kara.

Ya ce:

“Bangaren shari’a ta yi magana, shiyasa muke da kashe-kashen shari’a da suka hada da na kararrakin zabe da kuma na daukaka kara.
“Mun kai kara a kotun kararraki da daukaka kara kuma duk sun yi hukunci haka kuma Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe.
“Babu wani batun siyasa a ciki ko kuma wani shiri na musamman, abin da ya faru shi ne Kotun Koli ta fahimci shari’ar daban da sauran kotuna.”

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnan Abba ya faɗi gaskiya kan tsoma bakin Shugaba Tinubu a hukuncin kotun ƙoli

Wane zargi ake yi kan shari'ar Kano?

Chidi ya ce doka ai doka ce babu tantama a ciki, dole mu yabawa kotun saboda ta yi hukunci dai-dai da tsammanin ‘yan Najeriya, wannan ci gaba ne.

Ya ce hakan ya kara cire shakku kan cewa akwai sa hannun Gwamnatin Tarayya kan shari’ar zabukan jihohi, Naija News ta tattaro.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya samu nasara a Kotun Koli kan Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC.

NNPP ta yi martani kan hukuncin kotun koli

A wani labarin, Jam’iyyar NNPP ta yi martani bayan nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Koli.

Jam’iyyar ta ce nasarar ta bai wa ‘yan sha miyar siyasa kunya da suke neman yi wa gwamnan makirci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.