"Kwana 7 Na Yi Ban Barci": Gwamnan PDP Ya Fadi Yadda Cikinsa Ya Duri Ruwa Kan Hukuncin Kotun Koli

"Kwana 7 Na Yi Ban Barci": Gwamnan PDP Ya Fadi Yadda Cikinsa Ya Duri Ruwa Kan Hukuncin Kotun Koli

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nuna farin cikinsa kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar
  • Gwamnan ya bayyana cewa kafin yanke hukuncin sai da barcin kwana bakwai ya ƙauracewa idanunsa
  • Ya yi nuni da cewa ya yi fafutuka sosai domin ganin nasararsa ta zama gwamnan jihar ta tabbata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa kwana bakwai ya yi baya barci yana Abuja domin fafutukar hana ‘tsofaffin shugabannin Bauchi' ƙwace nasararsa a zaɓe.

Gwamnan ya kuma yabawa shugaban ƙasa, Bola Tinubu kan rashin sauraron tsofaffin shugabannin Bauchi da suka shaidawa shugaban ƙasar cewa shi barazana ce a gareshi, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Rundunar yan sandan Kano ta fitar da rahoton laifuka bayan hukuncin kotun koli

Bala Mohammed ya yi magana kan hukuncin kotun koli
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana halin da ya shiga kafin hukuncin kotun koli Hoto: Senator Bala Mohammed
Asali: Facebook

Bala Mohammed ya bayyana haka ne a gidan gwamnati da ke Bauchi a yayin wani gangamin nasara da aka shirya masa, inda ya kuma ce an bi doka da oda wajen shari'arsa, rahoton Daily Post ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamna Bala ya ce kan hukuncin kotun ƙoli?

A kalamansa:

"Ku (mutanen Bauchi) kun nuna min soyayya, kun ba ni amana kuma ba zan yi barci ba saboda kwana bakwai ban yi barci ba kuma na tabbatar an dawo mana da wannan nasara.
"Wasu sun haɗa kai da tsofaffin shugabannin Bauchi su je su ci gaba da yi min karya don ganin cewa shugabannin sama na kallo na a matsayin matsala, amma shugabannin suna da hanyoyin warware matsaloli.
"Ina godiya ga ɓangaren shari’a a Najeriya, musamman kotun ƙoli, ina godiya ga gwamnatin Shugaba Tinubu da ta yi imani da shugabanci na gari, inda ta ƙyale bin doka da oda ba tare da la’akari da ƙarya da munanan ayyukan da aka yi min ba.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnan Abba ya faɗi gaskiya kan tsoma bakin Shugaba Tinubu a hukuncin kotun ƙoli

"Ina godiya ga mataimakin shugaban ƙasa da dukkan abokan aikinmu a matakin tarayya. Ba wata ɓarna da za ta kai mu kasa,” inji shi.

Da yake sadaukar da nasarar da ya samu a kotun ƙoli ga al’ummar jihar, ya sha alwashin cewa ba zai bari wani mai “mugun nufi" ba daga ko’ina ya shugabanci jihar.

Gwamna Bala Ya Yabi Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana irin yadda ya ke kallon Shugaba Tinubu a zuciyarshi.

Gwamnan ya ce Tinubu ya na da matukar girma a wurinshi ganin yadda ya kau da kai a shari'ar zaɓen jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel