Mutum 8 Da Suka Zama Gwamnoni a Dalilin Hukuncin Kotun Koli Daga 2007 Zuwa Yau
- Kamar yadda kotun koli ta kan tsige Gwamnoni, hakan yana nufin akwai wadanda za a nada a mulki
- A sakamakon hukuncin kotun koli ne aka samu canjin lissafin masu mulki a jihohin Bayelsa da Zamfara
- A shekarun baya, ‘yan adawa sun karbe mulki daga hannun jam’iyyar PDP a Edo, Osun, Ekiti da sauransu
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - An yi ‘yan siyasa da suka zama gwamnoni a sanadiyyar hukuncin kotun koli wanda ita ce kotu mafi girma a dokar Najeriya.
A rahoton nan, Legit ta tattaro ‘yan siyasan da suka yi sa’ar samu mulki ta hanyar kotu:
Su wanene gwamnonin kotun koli?
1. Peter Obi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya koma kan kujerar mulkinsa a jihar Anambra ne da alkalan kotun koli suka tsige Mai girma Andy Uba a tsakiyar shekarar 2007.
2. Adams Oshiomhole
Adams Oshiomhole ya yi mulki a jihar Edo ne da kotu ta tunbuke Farfesa Oserheimen Osunbor bayan 'yan watanni a ofis a matsayin gwamna.
3. Kayode Fayemi
Dr. Kayode Fayemi yana sahun nan domin a dalilin tsige Olusegun Oni a kotu ne ya samu mulki, ya yi shekaru hudu a ofis kafin a doke shi a 2014.
4. Rauf Aregbesola
Osun ta na cikin jihohin da PDP ta rasa bayan zaben 2007, Rauf Aregbesola ya yi nasara a kotun koli a kan Mai girma Olagunsoye Oyinlola.
5. Bello Matawalle
Mukhtar Idris ake shirin za a rantsar a matsayin gwamna sai kotun koli ta karbe kujerun APC a Zamfara, a haka Bello Matawalle ya dare mulki
6. Hope Uzodinma
A zaben 2019, hukumar INEC ta ba Emeka Ihedioha nasara ne amma daga baya alkalai suka ce Hope Uzodinma na APC ne halattacen gwamna.
7. Douye Diri
Douye Diri ya sha kashi a hannun David Lyon a zaben gwamnan Bayelsa, kwatsam ana shirin rantsar da APC sai kotun koli ta soke nasarar Lyon.
8. Rotimi Amaechi
Rotimi Amaechi ya samu mulki ne a irin haka a 2007, duk da ba shi ya shiga zaben gwamnan Ribas ba, kotu ta ba shi nasara a jam’iyyar PDP.
Yadda Bola Tinubu ya samu mulki
A makon nan aka ji labari Femi Gbajabiamila ya fadi yadda aminan Bola Tinubu suka yi sanadiyyar zamansa shugaban kasa a 2023.
Hadimin fadar shugaban kasan ya ce wadanda suka yi aiki da Bola Tinubu a 1992 sun yi masa rana da ya tsaya takara a inuwar APC.
Asali: Legit.ng