Zamfara: Ban girgiza da hukuncin kotun koli ba – Inji Mukhtar Shehu Idris

Zamfara: Ban girgiza da hukuncin kotun koli ba – Inji Mukhtar Shehu Idris

Mukhtar Shehu Idris shi ne ya lashe zaben gwamnan jihar Zamfara, sai dai kafin a kai ga rantsar da mulki, kotun koli ta ruguza nasarar da APC ta samu saboda sabawa zaben tsaida gwani.

Alhaji Mukhtar Shehu Idris ya yi hira da Jaridar Daily Trust inda ya bayyana yadda ya ji a lokacin da aka yi fatali da kuri’a 534, 541 da shi da jam’iyyarsa ta samu ana shirin rantsar da gwamnoni.

Mukhtar Shehu Idris wanda aka fi sani da Koguna Gusau, ya ke cewa bai yi mamaki da Alkalan kotun koli su ka soke nasararsa daf da hawa mulki ba. Koguna ya ce dama can siyasa ta gaji haka.

Ba abu bane mai sauki, amma da jin labarin sakamakon kotu, sai na fara godewa Allah da mutanen Zamfara da su ka nuna mana soyayya da kauna da yarda da tafiyar mu da su ka yi.”

Tsohon Kwamishinan ya kara da cewa: “Jama’a sun yarda zan cigaba daga inda Mai gidana (Tsohon gwamna Abdulaziz Yari) ya tsaya na shawo kan matsalolin mutanen jihar Zamfara."

KU KARANTA: Gwamna Matawalle ya rike mani kudi na - Yari ya fara kuka

Koguna ya ce: “Daga nan sai na rike kai na, na kuma yi kokarin shawo kan jama’a domin su guji yin bore, na nuna masu cewa da Ubangiji ya nufe ni da yin gwamna, da babu wanda zai hana ni.”

‘Dan takarar na APC ya ke cewa Mai dakinsa ta yi hawaye da jin labarin sakamakon da kotu ta yanke. Shi kuma ya nuna mata cewa idan ta yi kuka, to ba ta godewa duk ni’imar Ubangiji ba.

Na fada mata cewa: “Na fito ne daga gidan da mu ke mu 33 a wajen Mahaifinmu. Daga wajen Mahaifiyarmu, mu 101 ne, da ‘Ya ‘ya da jikoki wajen Uwarmu, mu 528, amma Allah ya zabe ni...”

“…Har zuwa yau ba ta sake zubar da hawaye ba. Ita kuma Mata ta biyu, da ta samu labari, sai ta yi alwala, ta yi sallah, ta roka mani Allah samun karfin jurewa.” Yanzu ya ce su na jiran 2023.

.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel