APC Ta Bayyana Babban Dalilin da Ya Sa Ta Ke Samun Nasara a Zabuka, Ta Yi Alkawari Ga 'Yan Kasa
- Jam'iyyar APC ta bayyana irin shirin da take yi a ko wane zaben don tabbatar da nasarar ta ba tantama
- Kungiyar gwamnonin APC ta ce kullum jami'yyar a shirye ta ke don tunkarar ko wane zabe a ko wane lokaci
- Gwamnonin sun bayyana haka yayin ganawa da manema labarai bayan taronsu a Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar Gwamnonin Najeriya a jam'iyyar APC sun yi alfahari kan zaben da za a gudanar, Arise TV ta tattaro.
Gwamnonin karkashin kungiyar PGF sun ce kullum jami'yyarsu a shirye ta ke don tunkarar ko wane irin zabe a kasar a ko wane lokaci.
Nesa ta zo kusa: Kotun koli ta sanya ranar yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5
Mene APC ke cewa kan zabuka?
Gwamnonin sun bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja ta bakin shugabansu, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uzodinma ya ce jami'yyarsu a kullum jira take ko wane zabe ya zo saboda kullum a shirye suke kafin ma zuwan zaben, cewar Leadership.
Sai dai Uzodinma bai bayyana karara ko taron da suka gudanar ya shafi shirye-shiryen zaben da za a gudanar a wannan shekara ba.
Idan ba a mantaba, Hukumar INEC ta sanya 3 ga watan Faburairun wannan shekara a matsayin ranar gudanar zaben cike gurbin wasu kujeru.
Har ila yau, a ranar 21 ga watan Satumba za a gudanar da zaben gwamnan jihar Edo sai na jihar Ondo a watan Oktoba.
Wane alkawari APC ta yi?
Uzodinma ya ce wannan shi ne taronsu na farko a wannan shekara inda ya ce sun hadu ne don hada gwiwa da Gwamnatin Tarayya kan dakile matsalar tsaro.
Har ila yau, sun tattauna yadda za a hada kai don kawo cigaba mai dorewa a kasar baki daya.
Ya ce:
"Jamiyyarmu kullum a shirye ta ke don fafatawa a ko wane zabe, mun hada kai don mara wa gwamnatin APC baya.
"Za mu ci gaba da mara wa shugaban kasa, Bola Tinubu baya don kawo ci gaba a kasar baki daya."
Ganduke ya taya gwamnan APC murna
A wani labarin, shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya taya Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue kan nasara a Kotun Koli.
Ganduje ya roki jami'yyun 'yan adawa da su mara wa gwamnan baya don inganta rayuwar al'ummar jihar.
Asali: Legit.ng