Abin da Ya Sa Ba a Bukatar ‘Yan majalisa da Sanatoci 400 Inji Tsohon Sanata Shekarau
- Ibrahim Shekarau yana cikin masu ganin gwamnatin tarayya ta na kashe kudi masu yawa kan majalisu
- Tsohon Sanatan ya sake bada shawarar a soke majalisa guda ko akalla a rage adadin ‘yan majlisa
- Najeriya ta na amfani da ‘yan majalisar wakilan tarayya 360 da wasu sanatoci 109 a majalisar dattawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ibrahim Shekarau yana nan a kan ra’ayinsa na cewa ba a bukatar majalisar dattawa da ta wakilai a gwamnatin tarayya.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin Channels a ranar Talata, Ibrahim Shekarau ya soki tsarin majalisa da ake amfani da shi a Najeriya.
Majalisa biyu ko asarar kudi
Malam Ibrahim Shekarau wanda tsohon Sanata ne, ya yi tir da yadda Najeriya ta dauko salon Amurka na amfani da ‘yan majalisu biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya a majalisar dattawa yana da ra’ayin cewa majalisa guda ta isa, hakan zai sa a rage batar da kudi.
Ana so a rage kashe kudi a gwamnati
‘Dan siyasar ya bayyana wannan ne da aka nemi ya fadi ra’ayinsa a kan rage ayarin tafiya da shugaba Bola Tinubu ya yi cikin makon nan.
Rahoto ya zo cewa Shekarau wanda ya yi gwamna a Kano tsakanin 2003 da 2011 ya yabi gwamnatin tarayya a kan matakin da ta dauka.
Ba wannan ne karon farko da Shekarau ya yi irin wannan kira ba, kafin ya bar majalisar dattawa a 2023, ya fadi irin haka a talabijin.
Idan ta tsohon Ministan ilmin za a bi, za a rage adadin ‘yan majalisar tarayya a gwamnati.
An rahoto ‘dan siyasar yana yin kira ga majalisar tarayya tayi koyi da shugaba Bola Tinubu wanda yake kokarin rage kashe kudin gwamnati.
Majalisa: Matsayar Ibrahim Shekarau
"Na fada musamman bayan na yi aiki a can, gaskiya ba mu bukatar majalisu biyu.
Abin takaici, mun tafi mun kinkimo gaba daya tsarin Amurka mai dauke da majalisu biyu. Ban tunani muna bukatar haka, majalisa daya ta isa.
Ko dai a rage adadin ko kuwa a bar majalisa guda. Ina ganin hakan zai taimaka sosai a rage kudin da ake kashewa a gudanar da gwamnati."
- Ibrahim Shekarau
Gwamnati ta ci riba da NNPCL
An ji cewa sakamakon cire tallafin fetur, Kamfanin man NNPCL ya samu ribar Naira Tiriliyan 2.548 a karkashin jagorancin Mele Kolo Kyari.
A tarihin NNPCL tun 1977, ba a taba samun riba mai yawa irin na shekarar bara ba.
Asali: Legit.ng