N2.5tr: Kamfanin NNPC Ya Samu Ribar Da Ba a Taba Ji ba a Shekaru 47 a Zamanin Tinubu
- A shekarar da ta wuce watau 2022, kamfanin NNPC Ltd ya samu ribar fiye da Naira Tiriliyan 2.5
- Kafin zuwan dokar PIA, an yi shekara da shekaru, babu abin da NNPCL yake samu sai asara
- Bayanan da aka fitar a makon nan ya tabbatar da kamfanin man Najeriyan ya kafa tarihi a bara
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Kamfanin man Najeriya watau NNPC Ltd., ya sanar da cewa ya samu ribar N2.548tn a cikin shekarar 2022.
A ranar Talata, kamfanin NNPC Ltd ya bada sanarwar samun ribar da ta fi kowace tun da aka kafa ta a shekarar 1977.
An fara samun riba a kamfanin NNPCL
Punch ta ce kamfanin ya canza salo a Agustan 2021 bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a dokar PIA.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin gwamnatin Najeriyan ya koma kasuwanci da gaske musamman bayan tabbatar da cire tallafin man fetur a 2023.
Asara da ribar NNPCL a cikin shekaru 5
Bayanin da aka samu daga NNPCL ya nuna kamfanin man ya yi asarar N803bn a 2018.
Zuwa shekara mai zuwa ta 2019, sai asarar ta ragu zuwa 2019. A 2020 kuwa an samu ribar N287bn wanda ta canza lamarin.
A karkashin jagorancin Mele Kolo Kyari, a 2021, kamfanin man ya ci ribar N674.1bn wanda ya faru zuwa N2.458tr a 2022.
The Cable ta ce kamfanin zai fito da cikakken rahoton kudin da aka kashe da wanda aka samu a shekarar 2022 da ta gabata.
NNPCL na kama masu satar danyen mai
A sanarwar da aka fitar, kamfanin NNPCL ya bayyana cewa ya gano matatun tace mai na karya 52 a Neja Delta a mako guda.
A kokarin maganin masu satar arzikin Najeriya, kamfanin NNPCL ya bankado yadda ake fasa kaurin danyen mai a Akwa Ibom.
Rahoton ya ce NNPC ya gano miyagu na sace danyen mai a garuruwan Warri da Bayelsa, an kuma yi nasarar kama mutane 17.
Za a kara farashin fetur?
Kamfanin mai na kasa wanda aka fi sani da NNPCL yace ba a biyan tallafi kamar yadda bankin duniya da 'yan kasuwa su ke zargi.
Har yanzu ana sayen man fetur ne a kan N617-N690, duk da ikirarin cire tallafi tun 2023, wasu sun ce ya kamata farashin lita yt canza.
Asali: Legit.ng