Edo 2024: Jam'iyyar APC Ya Fara Siyar da Fom Ɗin Takarar Gwamna, Tsohon Minista Ya Lale N50m

Edo 2024: Jam'iyyar APC Ya Fara Siyar da Fom Ɗin Takarar Gwamna, Tsohon Minista Ya Lale N50m

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta fara sayar da fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara ga mambobinta masu nufin neman gwamnan Edo
  • Tsohon ƙaramin minista kasafi da tsare-tsaren kasa, Mista Clem Agba, shi ne ɗan takara na farko da ya lale N50m ya siya
  • A jadawalin ayyukan APC na zaben gwamnan Edo, za a rufe sayar da fom ɗin ranar 29 ga watan Janairu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Jam’iyyar APC ta fara sayar da fom din tsayawa takara da kuma nuna sha’awa ga mambobi jam’iyyar da ke neman kujerar gwamnan jihar Edo yau Laraba.

A ranar 16 ga watan Nuwamba ne za a gudanar da zaben gwamna a jihar Edo, rana daya da zaben gwamnan jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Yan sanda, sojoji da wasu hukumomin tsaro 5 sun karɓi kyautar motocin aiki sama da 100 daga gwamna

APC ta fara sayar da fom na takarar gwamnan Edo.
Jam'iyyar APC Ta Fara Siyar da Fam din Takarar Gwamnan Jihar Edo na 2024 Hoto: OfficialAPC
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC ta tabbatar da fara sayar da fom ɗin a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a kwanakin baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon minista ya sayi fom ɗin APC

Mista Clem Agba, tsohon karamin ministan kasafi da tsare-tsaren kasa shi ne dan takarar APC na farko daga jihar Edo da ya yanki fom ɗin a sakatariyar jam’iyyar ta kasa.

Mista Henry Idahagbon, tsohon Atoni-Janar kuma kwamishinan shari'a a Edo ne ya sayi fom din a madadin Agba.

Yadda APC ta tsara ayyukan zaben Edo

A jadawalin tsare-tsaren zaben gwamnan Edo da jam’iyyar APC ta fitar, za’a rufe sayar da fom din tsayawa takara da nuna sha’a da fom ɗin deleget ranar 29 ga watan Janairu.

Jam’iyyar APC za ta zabi dan takararta na gwamna a zaben fidda gwani da za a yi ranar 17 ga watan Fabrairu, 2024.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin gwamnonin jihohi 4 da za su san makomarsu a Kotun Koli a makon nan

APC mai mulki da tsaida kuɗin fom din nuna sha'awa kan N10m yayin da fom ɗin tsayawa takara kuma ya kai Naira miliyan 40.

Ƴan takara nakasassu da mata za su biya kuɗin fom ɗin nuna sha'awa ne kaɗai yayin da fom din takara kyauta ne a gare su.

Matasa masu shekaru 25 zuwa 40 za su sayi fom na nuna sha'awa da fom din takara a kan rangwamen kashi 50 cikin 100.

Wani jigon APC ya gaya mana cewa a halin yanzu jam'iyyarsu ta shirya tunkarar kowane irin zabe kuma ta lashe shi cikin sauki a kowane yanki na ƙasar nan.

Aliyu Zaharadden ya shaida wa Legit Hausa cewa:

"Idan ka duba a kullum APC ƙara gaba take yi, bana tunanin akwai wani zaɓe da zai gagare mu a kowane yanki. Abin da ya faru jiya a fadar shugaban ƙasa shaida ne.
"Mutum kamar Daniel Bwala yana faɗin zai iya dawowa APC, muna maraba da shi a ko da yaushe ya shirya, amma ina tabbatar maka jam'iyyar mu ta gama shiri."

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

Gwamna Makinde ya taimakawa jami'an tsaro

A wani rahoton kuma Gwamna Makinde ya sake rabawa hukumomin tsaro kyautar motocin sintiri sama da 100 a jihar Oyo.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi haka ne domin agaza musu wajen sauke nauyin da aka ɗora masu na tabbatar da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel