Yan sanda, Sojoji da Wasu Hukumomin Tsaro 5 Sun Karɓi Kyautar Motocin Aiki Sama da 100 Daga Gwamna

Yan sanda, Sojoji da Wasu Hukumomin Tsaro 5 Sun Karɓi Kyautar Motocin Aiki Sama da 100 Daga Gwamna

  • Gwamna Makinde ya sake rabawa hukumomin tsaro kyautar motocin sintiri sama da 100 a jihar Oyo
  • Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi haka ne domin agaza musu wajen sauke nauyin da aka ɗora masu na tabbatar da tsaro
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar, Adebola Hamzat, ya ba da tabbacin cewa zasu iya bakin kokarinsu wajen samar da kwanciyar hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Laraba, ya mika motocin sintiri sama 100 kyauta ga hukumomin tsaro daban-daban na jihar, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Hukumomin tsaro da suka amfana da kyautar motocin sun haɗa da ƴan sanda, sojoji, kwastam, gyaran hali, shige da fice da hukumar hana sha da fataucin kwayoyi (NDLEA).

Kara karanta wannan

Bayan kama 8, Asirin masu hannu a kisan bayin Allah sama da 150 ya ƙara tonuwa a arewa

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Gwamna Makinde Ya Bai Wa Hukumomin Tsaro Tallafin Motocin Sintiri Sama da 100 a Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Sauran hukumomin sun haɗa da rundunar haɗin guiwa da aka fi sani da Operation Burst, Amotekun da kuma hukumar kula da cunkoson ababen hawa ta jiha (OYRTMA).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Makinde na PDP ya ce gwamnatinsa ta kudiri aniyar taimaka wa jami'an tsaro wajen sauke nauyin da ke kansu ne duba da namijin kokarin da suka yi a sha'anin tsaro.

Da yake ƙara musu ƙarfin guiwa domin jajircewa wajen magance dukkkan masu tada zaune tsaye, Makinde ya roƙi shugabannin hukumomin da kar su ji kunyar faɗa masa bukatunsu a koda yaushe.

CP ya bada tabbacin tsaro a Oyo

Da yake magana a madadin shugabannin hukumomin tsaro, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Adebola Hamzat, ya ce ya yi matukar mamakin yadda gwamnatin jihar ta ƙara raba masu motoci.

A cewarsa ba a daɗe ba da gwamnatin Makinde ta siya masu motoci kyauta amma har ta ƙara tunanin tallafa musu da karin motocin aiki.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya kori dukkan kwamishinoni da hadiman gwamnatinsa a arewa, ya faɗi dalili

Hamzat ya bada tabbacin cewa jami’an tsaron za su yi amfani da motocin domin tabbatar da tsaro a lungu da saƙo na jihar Oyo.

Taron ya samu halartar shuwagabanni da jami’an hukumomin tsaro daban-daban, kamar yadda Pulse ta ruwaito.

Filato: An kama karin mutum 3 da ake zargi

A wani rahoton kuma Dakarun yan sanda sun kara kama waɗanda ake zargi da hannu a kisan bayin Allah sama da 150 a jihar Filato.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce an kama ƙarin mutum 3 masu safarar bindigu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel