Kotun Koli Ta Dauki Mataki Kan Karar APC da PDP Ta Neman Tsige Gwamnan LP
- Kotun ƙoli ta tanadi hukuncinta kan ƙarrrakin da ke neman tsige Gwamna Alex Otti na jihar Abia daga kujerarsa
- Kotun ƙolin mai alƙalai biyar ta cimma matsayar ne bayan ta kammala sauraron bayanai daga dukkanin ɓangarorin da ƙarar ta shafa
- Jam'iyyun PDP da APC da ƴan takarar gwamnan su na ƙalubalantar hukuncin da kotun ƙara ta yi na tabbatar da nasarar Alex Otti na jam'iyyar LP a zaɓen gwamna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A ranar Laraba kotun ƙoli ta tanadi hukunci kan ƙarar da jam’iyyun PDP da APC da ƴan takarar gwamnan su suka shigar kan zaɓen gwamna Alex Otti na jihar Abia.
Kotun mai alƙalai biyar sun tanadi hukunci har zuwa ranar da za a sanar da ɓangarorin bayan amincewa da dukkan bayanan da aka shigar a kan ƙarar, cewar rahoton Nigerian Tribune.
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Legas, ta yanke hukuncin bai ɗaya a watan Disamban 2023, inda tabbatar da nasarar da Otti na jam'iyyar Labour Party ya samu a zaɓen, inda ta ce nasararsa ta yi daidai da tanadin dokar zaɓe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa ƙararrakin da masu daukaka ƙarar suka shigar ba su da inganci, rahoton Gazettengr ya tabbatar.
Meyasa PDP da APC ke son a tsige Otti?
Jam’iyyar PDP da ɗan takararta, Okey Ahiwe da kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Cif Ikechi Emenikeand da jam’iyyarsa, a cikin karar da suka shigar sun bukaci kotun ƙoli da ta yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke.
Gwamna Alex Otti dai shi kaɗai ne gwamnan da jam'iyyar LP ta samu a babban zaɓen shekarar 2023 da ya gabata.
Kotu Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Otti
A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta zartar da hukunci kan ƙarar neman soke nasarar Gwamna Alex Otti na jam'iyyar LP, a zaɓen gwamnan jihar Abia.
Kotun ta tabbatar da nasarar da gwamnan ya samu tare da yin watsi da ƙararrakin da jam'iyyun APC da PDP suka ɗaukaka.
Asali: Legit.ng