Duk da Adawarsa, Mataki 1 da Shugaba Tinubu Ya Dauka Ya Jawo Atiku Ya Yaba Masa
- Bola Ahmed Tinubu ya samu yabon da bai saba samu ba daga babban ‘dan adawarsa, Atiku Abubakar
- ‘Dan takaran PDP a zaben 2023 ya ce an yi daidai da aka dakatar da Betta Edu domin ayi bincike a kan ta
- Atiku yana so ayi gyaran gaske a ma’aikatar jin-kai domin jami’an gwamnati su daina satar kudin talaka
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Atiku Abubakar yana ganin Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo a dalilin daukar mataki a kan Betta Edu da aka yi.
Jagoran adawar ya fitar da jawabi ta ofishin Phrank Shaibu a game da dakatar da Ministar jin-kai ta Najeriya, Dr. Betta Edu.
Hadimin Atiku sun yabi Tinubu
Mai taimakawa ‘dan takaran shugaban kasan a PDP wajen hulda da jama’a, ya ce an yi daidai da aka dauki matakin da ya dace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da haka Shaibu ya ce dakatar da Betta Edu domin bincike bai isa ba. Shi ma Daniel Bwala ya yabi gwamnati mai-ci a X.
Ceto talaka ko sace kudin talaka?
Atiku Abubakar yake cewa abin takaici ne a ce an koma amfani da tsarin ceto mutane miliyan 100 daga talauci wajen sata.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya zargi gwamnatocin Muhammadu Buhari da Bola Tinubu da amfani da tsarin ana barna.
Tun farko, Atiku ya ce bai dace Betta Edu ta rike wannan matsayi ba domin ba ta da kwarewar da za ta jagoranci ma’ikatar.
Ya aka yi Betta Edu ta zama Minista?
Jawabin ya ce bai dace a zabi tsohuwar kwamishinar a kan irinsu Imaan Ibrahim ba.
Vanguard ta ce Atiku ya zargi Femi Gbajabiamila da tsayawa Edu a lokacin da ake tantance ministoci a majalisar dattawa.
"Ka da a maida Betta Edu saniyar ware. Sai an bankado duk wadanda su ka amfana da dukiyar talakawan Najeriya, an yi bincike, an hukunta su.
Rashin imani da shedanci ne a saci kudi da sunan talaka."
Akwai bukatar gwamnati ta yi garmbawul a kan ayyukan ma’aikatar jin kai da sauran tsare-tsare domin sun zama ATM da POS na masu mulki.
- Pharank Shaibu
Binciken Dr. Betta Edu da Sadiyar Umar Farouk
Tsohon labari ne cewa ana zargin Ministocin da aka nada domin yakar talauci da satar miliyoyin kudin talakawan Najeriya.
Saboda a hana su ficewa daga Najeriya ana tsakiyar bincike, hukumar EFCC ta karbe fasfon Betta Edu da Sadiya Umar Farouk.
Asali: Legit.ng